’Yan Najeriya 52,000 za su sauke farali a 2025

Shugaban hukumar ya ce sun ɗauki matakan da za su daƙile dukkanin matsalolin yayin aikin Hajjin 2025.

’Yan Najeriya 52,000 za su sauke farali a 2025

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa an tanadar wa maniyyatan Najeriya 52,000 guraben aikin Hajjin na shekarar 2025.

Wannan na cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Bayanai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta fitar.

Ta ce hukumar ta riga ta biya kuɗin gurabe 26,287 na maniyyata, sannan ta tanadi wasu 26,000, da za a tabbatar da su gaba ɗaya kafin ranar 13 ga watan Fabrairu, 2025.

Domin cika wa’adin da Hukumar Aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta bayar, Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya tafi Makka domin ƙulla yarjejeniya.

Ya rattaba hannu kan yarjejeniyar a ranar 17 ga watan Janairu, 2025, bayan tuntuɓar shugabannin hukumar a jihohi da wakilin fadar shugaban ƙasa.

Shugaban ya tabbatar da ƙulla yarjejeniya da waɗanda za su kasance masu hidima tun da wuri don guje wa fuskantar tsaiko.

Wannan matakin yana da muhimmanci saboda ana sa ran fara aikin samar da biza ga maniyyata daga ranar 19 ga watan Fabrairu.

Shugaban NAHCON ya gode wa Mataimakin Shugaban Ƙasa, bisa goyon baya da taimakon da yake bai wa hukumar.

Ya ce hukumar za ta ɗauki matakan da suka dace don tabbatar da cewa maniyyata sun samu damar yin Hajji cikin sauki da kwanciyar hankali.

Ya kuma buƙaci su ci gaba da bibiyar kafofin sadarwa na NAHCON don samun sabbin bayanai.

’Yan Najeriya 52,000 za su sauke farali a 2025

An kama likita kan laifin yi wa ’yan bindiga magani a Katsina

Tirela ta murƙushe ɗaliba har lahira a Bauchi

Majalisun Tarayya sun amince da kasafin kuɗin N54.9trn na 2025