’Yan Najeriya ba ci-ma-zaune ba ne, taimakon yaki da talauci kawai suke bukata — Tinubu
Babu wani dalili da zai sanya mu zauna cikin talauci.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ’yan Najeriya ba ci-ma-zaune ba ne illa iyaka taimakon juna kawai suke bukata domin a yaki talauci.
BBC ya ruwaito Tinubu yana wannan furuci a kokarin jaddada aniyarsa ta jajircewa wajen gyara Najeriya.
- An kama matashin da ya sace ƙodar wani ya sayar a Abuja
- An fara ɗebe ƙauna daga samun masu rai a girgizar ƙasar Morocco
Tinubu ya bayyana cewa ’yan Najeriya masu ƙwazo ne, saboda haka babu wani dalili da zai sanya su zauna cikin talauci.
Shugaban Kasar ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar wasu dattawan Najeriya, da suka haɗar da jagororin jam’iyyun APC da PDP, a fadar shugaban ƙasa.
“Mu ba ci-ma-zaune ba ne, muna da arziƙi. Abin da muke buƙata shi ne taimakon junanmu, mu zama ‘yan uwa nagari. Ni ba shugaban ƙasar da zai ba da uzurririka ba ne,” kamar yadda mai magana da yawunsa ya bayyana.
“Zan yi aiki tuƙuru da manufofi masu kyau, da sadaukarwa da ƙwarin gwiwa don samar da arziƙi ga ’yan Najeriya, babu wani dalili da zai sanya mu zauna cikin talauci, ba za mu ci baya ba.”
Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa “Ba wani abu ba ne, yanzu muna fuskantar tsanani, amma daɗin na gaba.
“Za mu cimma muradunmu tare da cika burukan kakanninmu. Ina samun ƙwarin gwiwa daga ƴan ƙasar da nake mulki.”
Tawagar shugabannin sun ce sun yi amanar cewa zai ciyar da Najeriya gaba, zai kuma cika alƙawurran da yayi wa ’yan ƙasar.