’Yan Najeriya fiye da miliyan 40 va sa ajiya a vanki

Cibiyar bunkasa dabarun sarrafa kudi ta EFInA ta ce kimanin kasha 41.6 cikin 100 na ’yan Najeriya, wadanda suka cancanci yin  mu’amala da banki suna adana kudin su a gida, inda aka fitar da wannan adadi daga cikin mutum miliyan 96.4 a kididdigar shekarar 2016. Cibiyar EFInA, a binciken da ta gudanar tare da hadin […]

’Yan Najeriya fiye da miliyan 40 va sa ajiya a vanki

Cibiyar bunkasa dabarun sarrafa kudi ta EFInA ta ce kimanin kasha 41.6 cikin 100 na ’yan Najeriya, wadanda suka cancanci yin  mu’amala da banki suna adana kudin su a gida, inda aka fitar da wannan adadi daga cikin mutum miliyan 96.4 a kididdigar shekarar 2016.

Cibiyar EFInA, a binciken da ta gudanar tare da hadin gwiwar cibiyar kididdiga ta Najeriya (NbS) ya fitar da alkaluman yawan manya ’yan Najeriya (masu shekara 18 zuwa sama) da ya kai mutum miliyan 96.4.

binciken ya nuna cewa rashin hada-hadar sarrafa kudi ya yi kasa daga kasha 39.5 cikin 100 a shekarar 2014 zuwa 41.6 a shekarar 2016.

Sannan binciken ya bayyana yadda aka samu “nakasun  masu mu’amalar”: cewa masu mu’amalar sarrafa kudi a baya sun yanke wa kansu daina yin hada-hadar ne saboda matsanancin halin tattalin arziki, ko rashin amincewa da tsarin sarrafa kudin, ko kuma nisan da suka yi da wuraren hada-hadar kudin.

Rahoton ya danganta raguwar sha’awar (hada-hadar kudi) ga kalubalen  halin tattalin arziki na yanayin da aka fada a tsakanin shekarun 2015 zuwa 2016, wand aya haifar da illa ta kai tsaye ga karancin aikin yi da rashin isassun kudin ajiya da haiuhawar farashi, wanda babban tasirin illarsa ya fada kan makaskanta (a cikin  al’umma).

Muhimmin abin damuwa game da wannan bincike shi ne yadda rashin yin hada-hadar kudi ke bazuwa a sassan  kasar nan daban-daban.

Yankin Arewa maso Yamma ya samu karuwar rashin hada-hadar kudi daga kashi 56 cikin 100 a shekarar  2014 zuwa kashi 70 cikin 100. A Arewa ta tsakiya an samu karuwar rashin hada-hadar da kasha 33 cikin 100 a 2014 zuwa 39 cikin 100 a 2016.

An kimanta nakasun hada-hadar a yankin Kudu maso gabas da kasha 25 cikin 100 a shekoarar 2014 zuwa 28 cikin 100, snanan in an kwatanta da Kudu maso Yamma, wadda karancin yin hada-hadarta ya yi kasa daga kashi 25 cikin 100 a shekarar 2014 zuwa  kashi 18 ciklin 100 a shekarar 2016, al’amarin day a haifar wa yankin zarta kimar da aka yi masa hasashe na raguwar hada-hadar da kasha 20 cikin 100 nan da shekarar 2020.

Rakhoton ya nuna muhimmin ci gaban da aka samu a yankin Arewa maso Gabas, ionda karancin yin hada-hadar kudi ya ragu daga kasha 68 cikin 100  a shekarar 2014 zuwa kashi 62 cikin 100 a shekarar 2016, yayin da Kudu maso Kudu ya samu kyautatuwar al’amura, inda ragowar hada-hadarsa ta ragu kadan, wato daga kasha 33 cikin 100 a shekarar 2014 zuwa 31 cikin 100 a shekarar 2016.

Sai dai rahoton ya yi nuni da cewa samun rance na nan kan kimar kashi uku cikin 100 a tsakanin shekarun 2014 zuwa 2016, haka kuma fansho ma na nan kan kimar kasha biyar cikin 100 a tsakanin 2014 zuwa 2016.

binciken ya fito wa Najeriya dabarun shawo kan wannan matsala ta rashin hada-hadar kudi a bankuna, ta hanyoyi da dama, wadanda suka hada da kanan an inshore da fansho, wanda za a rika rabawa ta kafar sadarwar zamani ko a karba kai tsaye, sannan a himmatu wajen bunkasawa da kafa kananan sana’an ‘o’i da masana’antu da samar da amfanin gonad a kayayyakin amfanin gida da na daidaikun mutane, musamman wadanda ake amfani da su a gargajiyance, a kuma mayar da hankali kacokam kan al’amuran da suka shafi mata da matasa (wadanda ba a cika bas u muhimmanci ba), ta haka za a shawo kan asarar ayyuka da hada-hadar da ba a yi a harkokin tattalin arziki.