‘Yan Najeriya ku zabi wakilai masu ilimi- Sarkin Kano

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, ya bukaci ‘yan Najeriya da su zabi wakilai masu ilimi a zabuka na gaba. Sarkin ya bayyana hakan ne yayin yaye daliban jami’ar Nile ta Najeriya a Abuja wanda aka yi ranar Asabar. Ya kuma bukaci duk ‘yan Najeriya  da su tabbatar da sun sanya ‘ya’yansu a […]

‘Yan Najeriya ku zabi wakilai masu ilimi- Sarkin Kano

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, ya bukaci ‘yan Najeriya da su zabi wakilai masu ilimi a zabuka na gaba.

Sarkin ya bayyana hakan ne yayin yaye daliban jami’ar Nile ta Najeriya a Abuja wanda aka yi ranar Asabar. Ya kuma bukaci duk ‘yan Najeriya  da su tabbatar da sun sanya ‘ya’yansu a makarantu don saamun ingantaccen ilimi.

Jami’ar ta karrama Sarkin da digirin kimiyya.