’Yan Najeriya miliyan 120 ke cikin duhun rashin lantarki, inji Gwamnatin Tarayya

Daga dukkan alamu dai yanzu gwamnatin tarayya ta bara a yayin da ta bayyana gazawarta dangane da samar da wutar lantarki a kasar nan. Gwamnatin ta nuna cewa a halin da ake ciki ’yan Najeriya miliyan dari da ashirin ne suke cikin duhu. Minista a ma’aikatar wutar lantarki, Hajiya Zainab Kuchi ta bayyana wa manema […]

’Yan Najeriya miliyan 120 ke cikin duhun rashin lantarki, inji Gwamnatin Tarayya
’Yan Najeriya miliyan 120 ke cikin duhun rashin lantarki, inji Gwamnatin Tarayya

Daga dukkan alamu dai yanzu gwamnatin tarayya ta bara a yayin da ta bayyana gazawarta dangane da samar da wutar lantarki a kasar nan. Gwamnatin ta nuna cewa a halin da ake ciki ’yan Najeriya miliyan dari da ashirin ne suke cikin duhu.
Minista a ma’aikatar wutar lantarki, Hajiya Zainab Kuchi ta bayyana wa manema labarai a gidan gwamnati, jim kadan da kammala taron majalisar zartarwa a shekaranjiya Laraba.
Wannan bayani na minista ya zama akasi a kan jawabin da Shugaba Goodluck Jonathan a makon da ya gabata inda ya nuna irin cigaban da gwamnatinsa ta samu a cikin shekaru biyun da suka shige a sassa daban-daban na gudanar da mulkinta.
Ministar ta yi ikirarin cewa ’yan Najeriya miliyan arba’in ne kawai suke samun wutar lantarkin daga cikin kimanin mutum miliyan dari da sittin na al’ummar kasar, duk da irin dimbin kudin da aka kwarara a yankin samar da wutar lantarkin.
Ta ce duk da yake hakkin gwamnati ne ta ba ’yan Najeriya wutar lantarki, amma hakan ba za ta samu ba, dole sai an hada da sashen kasuwanci.  
Minista Kuchi ta ce, “Muna da ’yan Najeriya miliyan dari da sittin a yanzu, kuma mun ba mutum miliyan arba’in kawai wutar lantarki.  A lissafi ke nan mutum miliyan dari da ashirin suna cikin duhu, ta yadda dole sai dai su nema.  Amma muna nan muna ta neman hanyoyin samun mafita a kan wannan al’amari.  Sai dai kuma muna ganin hanya daya tilo da za mu iya samar da wannan wutar lantarki ita ce waiwayar ’yan kasuwa masu zaman kansu (Independent Power Projects -IPPs).  Mun dade muna cewa ba ma son mulkin mallaka, saboda haka muke son ’yan gida, ’yan Najeriya su kasance su ke mallakar irin wannan dandali na kasuwanci.  In har za a sayar da ruwa a titi, to za a iya samar da lantarkin saye fiye da ruwan, saboda kowa na bukatarsa a kowane lokaci, dare ko rana.
“Saboda haka,idan muka hada karfi da karfe, muka giggina ire-iren wannan dandali don samar da wutar, za mu fahimci ba gwamnati ce kadai take da bukatar kudin gudanarwa ba.  Irin karfin wutar lantarkin da muke bukatar samarwa ta sa bamban a fuskoki da dama, wadanda kowane dan Najeriya yana da damar samarwa.  Akwai hasken rana; akwai iska; akwai ruwa, wadanda suke ko’ina ga su nan kyautar Allah. Abin da kawai muke bukata shi ne samar da farfajiyar tatso wutar lantarki, mu yi da gaske, mu yi tsayin-daka don gudanar da kasuwanci a wannan fanni, sai mu ga kudi na kwararowa cikin aljihunmu.  Gwamnati ta yi kokari.  Muna da duk hanyoyi samun karsashi, musamman ta fuskar waiwayar kwal, wanda tun farko da shi akan samar da karfin wutar lantarki”.
Tun farko, Ministan Lantarki, Furofesa Chinedu Nebo sai da ya suranta lamarin kamar mafarki ko tatsuniya, inda ya zargi kasancewar hakan a kan bannar ruwan sama da abin da ya yi kama da shi, sai kuma mabarnata da ’yan sama-da-fadi da masu hana ruwa gudu da kuma jinkirin rashin mayar da sha’anin zuwa kasuwa.