’Yan Najeriya miliyan 15 ne ke shan gurbataccen ruwa-Asusun UNICEF

Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya wanda a takaice ake kira UNICEF ya bayyana cewa kimanin ’yan Najeriya miliyan 57 ne ba su iya samun tsaftaccen ruwa . Sannan asusun ya kara da cewa kimanin mutum miliyan 15 ne a kasar suke shan ruwan gulbi ko kogi ko ruwan da ake ban […]

’Yan Najeriya miliyan 15 ne ke shan gurbataccen ruwa-Asusun UNICEF

Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya wanda a takaice ake kira UNICEF ya bayyana cewa kimanin ’yan Najeriya miliyan 57 ne ba su iya samun tsaftaccen ruwa .
Sannan asusun ya kara da cewa kimanin mutum miliyan 15 ne a kasar suke shan ruwan gulbi ko kogi ko ruwan da ake ban ruwan noman rani da shi.
Kwararre a Fannin Ruwa da Tsafta na Asusun UNICEF, Mista Moustapha Niang, shi  ne ya bayyana haka a tattaunawar tsaftace hannu da Asusun UNICEF da hadin gwiwar kasashen turai suka yi da manema labarai a garin Uyo da ke jihar Akwa-Ibom.
Moustapha ya ce kinanin yara dubu 45 ’yan kasa da shekaru biyar ke mutuwa duk shekara sakamakon  kamuwa da cututtukan da gurbataccen ruwa ke haddasawa.