’Yan Najeriya miliyan 19 za su yi fama da yunwa a 2022 —Rahoto

Mutum miliyan 14 na fama da karancin abinci a halin yanzu a Najeriya

’Yan Najeriya miliyan 19 za su yi fama da yunwa a 2022 —Rahoto

Wani bincike da cibiyar Cadre Harmonisé (CH) ta gudanar da hadin gwiwar Gwamnatin Tarayya ya nuna cewa daga yanzu zuwa watan Agusta, mutanen da za su yi fama da karancin abinci a za su karau zuwa miliyan 19.4 a jihohi 21 a Najeriya.

Cibiyar da ke bincike kan karancin abinci a kasashen Yammacin Afirka da yankin Sahel ta yi binciken ne tare da Ma’aikatar Noma ta Najeriya, Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya da kuma Hukumar Noma da Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya.

Rahoton ya bayyana cewa mutum 416,000 daga cikin wadanda matsalar karacin abinci za ta shafa a bana ’yan gudun hijira ne a jihohin 21 da Birnin Tarayya, Abuja.

Jihohin da matsalar za ta shafa sun hada da Kano, Borno, Zamfara, Katsina, Sakkwato, Neja, Kebbi, Kaduna, Yobe, Adamawa, Bauchi, Binuwai. Sauran su ne Taraba, Abiya, Kuros Riba, Edo, Enugu, Gombe, Jigawa, Filato, Legas da kuma Abuja.

Binciken da CH ta gudanar kan wata ukun farkon 2022 ya nuna a halin yanzu mutum 14.4 na fama da karancin abinci a jihohin, tun daga watan Mayun 2021. Daga cikinsu kuma, mutun 385,000 ’yan gudun hijira ne a jihohin.

Rahoton ya alakanta matsalar karancin abinci da rashin tsaro, musamman a yankin Arewa Maso Gabas, hauhawar farashin kayan masarufi, da raguwar kudaden shigan magidanta a sakamakon bullar cutar COVID-19.

Da yake gabatar da rahoton a Abuja ranar Juma’a, wakilin Hukumar Noma da Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya da kasashen ECOWAS, Mista Fred Kafeero, ya bukaci a yi gyara ga tsarin samar da abincin Najeriya a muradunta na 2030.

Kafeero, wanda Farfesa Salisu Mohammed ya wakilta a taron ya roki Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da binciken na CH a tsare-tsarenta na kasa, ciki har da shirin samar da abinci.

A nasa bangaren, Babban Sakataren Ma’aikatar Noma da Raya Karkara ta Tarayya, Dokta Ernest Umakhihe, ya ce gudanar da biciken ya zama dole ne domin fahimtar ainihin abubuwan da ke haddasa matsalar karanicn abinci da rashin lafiyayyen abinci a kasar.

“Kada mu manta cewa matsalar rashin tsaro na ci gaba da barazana ga kasarmu da ma kokarin samar da wadataccen abinci a kasar,” inji shi.