’Yan Najeriya miliyan 31.8 na fuskantar ƙarancin abinci — Rahoto

Rahoton ya ce matsalar ta samo asali ne daga cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi.

’Yan Najeriya miliyan 31.8 na fuskantar ƙarancin abinci — Rahoto

Aƙalla mutum miliyan 31.8 ne, ke fuskantar matsalar ƙarancin abinci, wanda hakan ke ƙara tsananta matsalar rashin lafiya a tsakanin mata da ƙananan yara a Najeriya.

Wannan na cikin wani rahoton ‘Cadre Harmonise’ na 2024, wanda ya bayyana cewa hauhawar farashin kayan abinci ya samo asali daga cire tallafin man fetur da kuma matsalolin tsaro.

Rahoton ya bayyana cewar hakan ya jefa dubban ’yan Najeriya cikin tsaka mai wuya.

Cikin wata sanarwa da daraktar yaɗa labarai ta Ma’aikatar Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsaren Tattalin Arziƙi, Julie Osagie-Jacobs, ta bayyana hakan.

Ta ce abokan hulɗarsu irin su FAO, GAIN, GIZ, da Agsys sun bayyana hakan ne a taron duba aiwatar da tsarin abinci a Najeriya.

Julie, ta bayyana cewa magance matsalar tsaro game da abinci na buƙatar haɗin gwiwa daga sassa daban-daban.

Ta ce dole ne a yi aiki tare don magance dukkanin matsalolin a lokaci guda.

Har wa yau, ta jaddada cewa ƙungiyoyin al’umma da kuma masu zaman kansu suna da muhimmanci wajen kawo dabarun samar da abinci.

Abokan hulɗar sun yi alƙawarin tallafa wa sauye-sauye a tsarin abinci na Najeriya.

Babban Sakatare a ma’aikatar, Dokta Emeka Vitalis Obi, ya ce manufar taron, shi ne duba ci gaban ayyukan tsarin abinci da kuma duba sabbin abubuwa daga sassa daban-daban na gwamnati.

Ya gode wa abokan hulɗar irin su GIZ saboda goyon bayansu na inganta tsarin abinci na Najeriya, inda ya jaddada cewa haɗin gwiwarsu zai kawo sabbin mafita.

Dokta Sanjo Faniran, Shugaban Tsare-Tsaren Abinci a Najeriya da Daraktan Harkokin Ci Gaban Al’umma a Ma’aikatar Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsaren Tattalin Arziƙi, ya kuma gode wa dukkanin masu ruwa da tsaki saboda jajircewarsu wajen ci gaban tsarin abinci a ƙasar nan.

Mai hannu ɗaya da ke sana’ar faskare

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru da kaso 33 a Najeriya — NBS

Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar rushe Hukumar EFCC