’Yan Najeriya Miliyan 6.3: Likita 1
kungiyar Likitocin Najeriya ta bayyana tana da mambobi dubu 27 da suka yi rijista da ita. A yanzu an yi kiyashin yawan mutanen Najeriya ya kai miliyan 170. Mawuyacin halin da ake ciki a bangaren kiwon lafiya a bayyane yake, idan aka yi lissafin yawan jama’a da kuma na likitocin da ake da su a […]
kungiyar Likitocin Najeriya ta bayyana tana da mambobi dubu 27 da suka yi rijista da ita. A yanzu an yi kiyashin yawan mutanen Najeriya ya kai miliyan 170. Mawuyacin halin da ake ciki a bangaren kiwon lafiya a bayyane yake, idan aka yi lissafin yawan jama’a da kuma na likitocin da ake da su a kasar nan. Hakan yana nufin likita 1 ne ke duba lafiyar mutane miliyan 6 da dubu 300 a Najeriya. Majalisar dinkin Duniya ta fitar da ka’idar akalla likita 1 ya rika duba lafiyar mutane dubu, idan kuwa haka ne, ya kamata a samu likitoci 170,000 a Najeriya.
Tsohon Shugaban kungiyar Likitoci na Najeriya, Dokta Osahon Enabulele ne ya bayyana yawan likitocin da ake da su a kasar nan, a lokacin wani zama da kungiyarsu ta yi a Eket makon jiya.
Ya ce hakan ne don gwamnati ta fahimci kalubalen da ke gabanta. Ya ce rashin likitoci ne ya haifar da babban gibi a bangaren lafiya a kasar nan. Hakan ya faru ne saboda fiye da shekara 30 ba a kara yawan makarantun da suke aikin koyar da kiwon lafiya a kasar nan ba.
Baya ga haka ko makarantun da suke koyar da aikin kiwon lafiya ma ba a inganta su ba, wasu kuma an mayar da su kamar na kwantiragi. Misali a Jami’ar Ahmadu Bello shekara biyu ke nan ba a dauki daliban da ke karatun koyon aikin likita ba.
Rashin samun isassun likitoci na daya daga cikin matsalolin da suke haifar da karancin likitoci a kasar nan. Likitoci kadan din da suka rage a Najeriya na fuskantar matsalar karancin kayan aiki, hakan ya sanya da yawansu suka rika koma wa kasashen wajen don ci gaba da aiki. Hakan ya haifar da karancin likitoci a kasar nan.
An ta’allaka tabarbarewar asibitocin lafiya matakin farko a wuyan tsohon Ministan Lafiya Farfesa Olikoye Ransome Kuti, har masu sharhi suka ce hakan ne ya sanya asibitocin lafiya mataki na biyu da na uku suka tabarbare, baya ga karancin makarantun da suke koyar da aikin lafiya.
Makasudin samar da asibitocin lafiya matakin farko irin su asibitin sha-ka-tafi da cibiyoyin kula da lafiya shi ne, don magance cututtuka irin su Maleriya da ciwon Typhoid da amai da gudawa da kwalara da tari da gonoriya da sauransu, amma a yanzu manyan asibitocin lafiya a mataki na biyu da na uku ne suke aiki, don magance wadannan cututtuka. Wadannan manyan asibitoci ya kamata su rika yin tiyata da kuma magance manyan cututtuka ne.
Ya zama dole gwamnati ta fito da tsarin da zai magance karancin likitoci da samar da asibitocin da za su rika aikin magance kananan cututtuka. Wannan kuwa ya hada da gina makarantun da za su rika koyar da aikin lafiya, sannan a inganta makaratun da ke koyar da karatun kiwon lafiya, hakan zai samar da guraben dalibai masu karatun kiwon lafiya. Zai kuma sa a rika samun likitoci a kasar nan duk shekara.
Don kuma a magance tserewar likitoci zuwa kasashen ketare, sai a samar da isassun kayan aikin masu inganci. Idan har gwamnati za ta samar da dukkan wadannan abubuwa, to zai yi wahala a rika rudar likitocinmu da wani abu don su yi aiki a kasashen waje.
Ya kamata kungiyar Likitocin Najeriya ma ta taimaka wajen dakile yajin aikin da take yawaita yi, wanda hakan na kara kawo tabarbarewar harkar lafiya a kasar nan. Idan komai ya inganta jama’a za su daina tururuwar zuwa kasashen waje don a duba lafiyarsu, ko kuma su fita don yin jinya.
Ya zama dole a inganta asibitocin sha-ka-tafi da cibiyoyin kula da lafiyar al’umma da suke kauyuka da kuma birane, idan an yi hakan za a rage cunkoson da ake samu a manyan asibitocin lafiya a mataki na biyu da na uku. Domin ba za a rika zuwa wadannan asibitocin don karamin ciwo ba.