’Yan Najeriya miliyan 60 na fama da tabin hankali
An bukaci sake fasalin kula da lafiyar ’yan Najeriya masu fama da tabin hankali musamman a karkara.
Alkaluma sun nuna yanzu haka ’yan Najeriya sama da miliyan 60 ne ke fama da tabin hankali nau’i daban-daban a sassan kasar.
Shugaban Kungiyar Likitocin da ke kula da masu fama da cutar tabin hankali a Najerya, Farfesa Taiwo Obindo ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ranar Lahadi a Abuja.
Obindo wanda ke jagorancin Tsangayar Kula da Masu Fama da Tabin Hankali a Cibiyar Horar da Likitoci ta Afirka ta Yamma da ke Najeriya, ya bayyana cewar halin kula da masu fama da cutar tabin hankali a Najeriya ya tabarbare, ganin yadda alkaluma suka nuna cewar kasar na dauke da mutane sama da miliyan 60 da ke fama da matsalar.
Masanin ya bayyana cewa, abin takaici shi ne kashi 90 na wadannan mutane da ke fama da matsalar ba su da hanyar zuwa asibiti domin samun kula daga likitoci, sai kashi 10 kacal wadanda ba su da yawa.
Daga cikin matsalolin da masanin ya gabatar a matsayin wadanda ke hana masu fama da cutar samun magani, sun hada da rashin bayani dangane da abinda ke haifar da cutar da kuma yadda ake kula da ita.
Ya ce akwai kuma yadda hukumomin Najeriya ke yi wa matsalar rikon ko-in-kula da kuma al’adar wasu ’yan Najeriya dangane da matsalar, sai kuma karancin kwararrun likitocin da ke kula da masu fama da cutar.
Obindo ya kuma bayyana karancin asibitocin da ake kula da masu fama da cutar, ganin cewar akasarin jihohin da suke da su, sun sanya su ne a birane, yayin da sama da kashi 60 na jama’ar Najeriya ke zama a yankunan karkara.
Masanin ya bukaci sake fasalin kula da lafiyar ’yan Najeriya domin sanya shirin kula da masu fama da tabin hankali a cikin ayyukan kananan asibitocin da ke yankunan karkara.