’Yan Najeriya miliyan 64 na fama da tabin hankali – Farfesa Nebo

Tsohon Ministan Wutar Lantarki Farfesa Chinedu Nebo ya nuna damuwa kan yadda Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi ba su bayar da kula ga ’yan Najeriya kimanin miliyan 64 da suke fama da tabin hankali.Farfesa Nebo ya bayyana haka ne a wurin Lacca ta Biyu da Asibitin Mahaukata na Tarayya da ke Enugu da Kwalejin Nas-Nas […]

’Yan Najeriya miliyan 64 na fama da tabin hankali – Farfesa Nebo
’Yan Najeriya miliyan 64 na fama da tabin hankali – Farfesa Nebo

Tsohon Ministan Wutar Lantarki Farfesa Chinedu Nebo ya nuna damuwa kan yadda Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi ba su bayar da kula ga ’yan Najeriya kimanin miliyan 64 da suke fama da tabin hankali.
Farfesa Nebo ya bayyana haka ne a wurin Lacca ta Biyu da Asibitin Mahaukata na Tarayya da ke Enugu da Kwalejin Nas-Nas na Afirka ta Yamma suka shirya a ranar Litinin da ta gabata.
Farfesa Nebo wanda ya yi magana kan batu mai taken: “Hauka da Lafiyar kwakwalwa a Najeriya: kalubale da Mafita,” ya ce, a cewar malaman kiwon lafiya daga cikin mutum miliyan 160 ko makamancin haka, ’yan Najeriya miliyan 64 suna fama da wani nau’i na tabin hankali da ke bukatar kula.
Farfesa Nebo, wanda tsohon Shugaban Jami’ar Najeriya da ke Nssuka ne ya ce, a yayin da gwamnati ke taka rawa wajen kula da lafiya daga tushe, babu abin da take yi wajen magance matsalolin tabin hankali.
Ya ce ba a kuma fahimtar da ’yan Najeriya yadda ya kamata game da cututtukan da suka shafi kwakwalwa, “Yanzu haka ’yan Najeriya da dama na fama da matsalolin rayuwa ciki har da talauci da tsabagen rashin aiki da sauran matsalolin rayuwa. Kuma lamarin yana dada muni idan aka lura da cewa ana fama da karancin sani kan illar lafiyar kwakwalwa da yadda za a magance ta a daidai lokacin da ake samun karuwar dimbin jama’ar da kwakwalwarsu ke motsuwa,” inji shi.  
Ya bayyana cewa abubuwan da suke kawo tabin hankali sun hada da gado da shaye-shaye da damuwa da kuma matsi. Sai ya musanta tunanin da wasu ’yan Najeriya ke yin a cewa aljannu ne ke jawo tabin hankali ga mutane, inda ya alkanta hakan da camfi da al’ada.
Farfesa Nebo ya bukaci ’yan Najeriya su yi watsi da wannan tunani su fuskanci gaskiyar lamari kamar yadda ilimi ya tabbatar a zamanance wanda ya nuna cewa gajiya da matsi a matakai daban-daban suka fi jawo tabuwar hankali.
Tsohon Ministan ya bukaci a samar da kudi don gudanar da bincike da horar da ma’aikatan kula da lafiyar kwakwalwa, tare da kiran a samar da tsarin kiwon lafiyar kwakwalwa a matakan karkara da shigar da kula da kiwon lafiyar kwakwalwa a tsarin kula da lafiya daga tushe inda za a rika sake nazarin dokokin kula da lafiyar kwakwalwa a duk shekara.
Babban Daraktan Asibitin Mahaukata na Tarayya da ke Enugu, Dokta Jojo Onwukwe, ya ce asibitin yana da ma’aikata kusan dubu daya da suka hada da kwararrun likitoci guda takwas da Nas-Nas masu kula da mauhaukata fiye da 400 da kuma wasu likitoci 27.