’Yan Najeriya mu kyautata dabi’unmu don samun makoma tagari – Dokta Oyakhire

Tsohon Gwamnan Jihar Taraba da Oyo, kuma Tsohon Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan Sandan Najeriya, Mai ritaya Dokta Aman Yarima Oyakhire, ya bayyana bukatar ganin al’ummar kasar nan su gyara halayyarsu, ta bangaren siyasa da addini, domin dorewar zaman lafiya. Dokta Aman Yarima Oyakhire, ya fadi wannan ne a zantawarsa da wakilin Aminiya a garin […]

’Yan Najeriya mu kyautata dabi’unmu don samun makoma tagari – Dokta Oyakhire
’Yan Najeriya mu kyautata dabi’unmu don samun makoma tagari – Dokta Oyakhire

Tsohon Gwamnan Jihar Taraba da Oyo, kuma Tsohon Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan Sandan Najeriya, Mai ritaya Dokta Aman Yarima Oyakhire, ya bayyana bukatar ganin al’ummar kasar nan su gyara halayyarsu, ta bangaren siyasa da addini, domin dorewar zaman lafiya.

Dokta Aman Yarima Oyakhire, ya fadi wannan ne a zantawarsa da wakilin Aminiya a garin Benin fadar Mulkin Gwamnatin Edo, inda ya fara da bayanin cewa: ‘’Lallai muna cikin lokacin da ake bukatar mu zabi nagartattun jagorori, a gaskiya wannan ita ce ainihin shekarar da ‘yan Najeriya za su zabi Shugabanninsu. Don haka ya kamata mu gyara halayyarmu, ta yadda za a samu zaman lafiya. Muna son mu zabi wanda zai kawo canji mai amfani a Najeriya, ba irin zaman duhu da muka fada a ciki na tsawon shekaru 15 da suka shude ba.’’
Kuma da ya juya akan batun ‘yan Siyasa Yarima Oyakhire ya ce, shugabanni ‘yan siyasa su ma akwai bukatar su canja irin dabi’unsu na ko in kula da suke yi da sha’anin shugabanci a kasar nan, wannan yana kara mayar da mu baya ba kadan ba.
“Don haka ina Shawartar Shugabannin da su kasance nagartattu da za’ayi koyi dasu amma masu hatsa wutar fitina ko buda wata kafar tashin hankali ba, domin su ne za su zama shugabanninmu nan gaba,” inji shi.
Dokta Akhire ya karkare da cewa: ‘’Akwai bukatar ‘yan Najeriya su kasance masu nuna kyakkyawar dabi’a irin na ‘yan kasa masu kishi da jajircewa, domin tsamo kasar mu daga kangin bala’in rayuwa, kamar yadda muke gani, muke ciki a halin.”
“Lallai dage zaben Najeriya zuwa watan Maris da Afrilu, mutane da dama ba su ji dadin shirin ba, amma fatarmu ita ce, Allah ya sa hakan ya zama mafi alheri ga makomar Najeriya da al’ummanta,’’ inji shi.