’Yan Najeriya na cikin mawuyacin hali – Dokta Lema Jibril
Dokta Lema Jibril tsohon dan siyasa ne a kasar nan kuma sanannen manomi dan kasuwa. Ya taba tsayawa takarar Shugaban kasa a karkashin rusasshiyar Jam’iyyar NRC. A zantawarsa da manema labarai a gidansa ya ce ’yan Najeriya suna cikin mawuyacin hali sakamakon rashin aikin yi a tsakanin al’umma: Aminiya: A matsayinka na tsohon dan takarar […]

Dokta Lema Jibril tsohon dan siyasa ne a kasar nan kuma sanannen manomi dan kasuwa. Ya taba tsayawa takarar Shugaban kasa a karkashin rusasshiyar Jam’iyyar NRC. A zantawarsa da manema labarai a gidansa ya ce ’yan Najeriya suna cikin mawuyacin hali sakamakon rashin aikin yi a tsakanin al’umma:
Aminiya: A matsayinka na tsohon dan takarar Shugaban kasa ka gamsu da yadda siyasar kasar nan ke gudana?
Wannan tafiya ban iya cewa daidai ne ko bai daidai ba. Saboda matsalar da kasa ke ciki kowa ya dauka komai ya lalace, zan iya cewa kusan haka din ne. Amma ai ba siyasa ce ta kawo hakan ba. In ka dauki duniya gaba daya abin da ke faruwa ke nan na rashi da talauci da fakiranci da komai. Har babbar kasar duniya Amurka tana fama da shi, Ingila da Jamus da Faransa duk suna da shi.
Yanzu a kasashen Girka da Spain marasa aikin sun kai kusan kashi 30 cikin 100 . Sai dai namu ya kai kusan kashi 50 cikin 100. Wannan wani bala’i ne ya auka wa duniya gaba daya, amma kuma ruwan da ya doke ka, Hausawa sun ce shi ne ruwa. Saboda haka mu namu za mu ji da shi kawai. Sai an sake lale yadda abubuwan suka tabarbare a Najeriya wajen tafiyar da abubuwan yau da kullum.
Ana cikin wani mugun hali na mawuyacin halin rayuwa, mutane babu kudi, babu asibiti ba ruwan sha ba ma karatu. Dole sai an sake lale. Kodayake zabe na zuwa idan ba ku zabi wadanda suka dace ba wannan ruwanku.
Aminiya: Ke nan dimokuradiyya ta yi amfani ko ba ta yi ba?
Ta yi amfani kwarai da gaske, ai dimokuradiyyar ke ba mu damar mu tattauna a tantance sannan mu fada wa juna gaskiya kan yadda abubuwa ya kamata su zama. In da babu dimokuradiyyar hakan ba zai yiwu ba, a mulkin dimokuradiyya sai ka fadi albarkacin bakinka yadda ya yi maka. Shi ne dadin dimokuradiyyar.
Aminiya: Ka taba tsayawa takarar mulkin kasar nan a tsohuwar Jam’iyyar NRC kusan shekara 20 da suka wuce. A shekarun nan ka yi shiru ba ka cewa komai, ga shi kuma nan da shekara biyu za a sake zabe a kasar nan. Ko ’yan Najeriya za su ji daga gare ka?
Zan ci gaba da yadda nake yi a shekarun da suka wuce, ai mulki na Allah ne kuma yana hannun jama’a. Jama’a sun ga yadda wadannan mutane suka tafiyar da al’amura shekara 15 ko 20 da suka wuce. Idan ba a yi lissafi aka waiwayi baya ba cewa shin me suka yi mana na alheri ko akasinsa ba. To, shi ne mutane za su tantance su ga me ya kamata su yi.
Sun sha wuya ne ko sun samu ci gaba ne a cikin shekara 20 din nan da suka wuce ko kuwa? Kuma mutanen nan me suka haddasa na samun ci gaba ko sha’anin inganta noma ko kiwo ko kasuwanci da masana’antu. Sai a tambayi masu cewa a zabe su me suka yi domin inganta wadannan fannoni a kasar nan? Abin da ya kamata jama’a su duba ken an domin su san amfaninsu a siyasance.
Aminiya: Kana ganin wannan siyasa ta amfani Arewa kuwa?
Eh, to ni naïf son in yi magana ne a kan kasa baki daya ba wani yanki daya kadai ba. Zan iya cewa kusan matsalolin kasar nan sun shafi kowane yanki na kasar nan. Sai dai kawai in ce abin bakin ciki shi ne a nan Arewa muna fama ne da rashin tsaro da kuma rikicin addini da na kabilanci.
In bayan wannan zan iya cewa duk matsalolinmu daya ne. Kuma duk muna da manufofinmu daya ne wajen son mu ga mun kyautata wa ’yan kasar nan baki daya. Gaskiya ne cewa a nan Arewa akwai matsalar siyasa sai dai mun fi fama da rikicin addini a yankin nan. Kuma insha Allahu duk wadannan matsaloli za a magance su.
Babu yadda za a ce kowa ya gamsu da yadda ake mulkin nan. Ni dai na gamsu da yadda wasu abubuwa ke gudana a kasar nan. Sai dai kawai zan iya cewa babban kalubale da ke damun kasar shi ne rashin aikin yi. Wannan wata matsala ce da ke matukar damun kasar nan. Alkalumar gwamnati suna cewa rashin aikin yi bai fi kashi 25 ba, amma gaskiyar batun shi ne rashin aikin yi ya kai kashi 50 a kasar nan.
Ka ga wannan abin bakin ciki ne sosai, shi ya sa muke fama da rashin tsaro da yawan aikata laifuffuka a cikin al’umma, saboda mutanen da ya dace a ce suna aiki ba su yi. Dole ne mu wayar da kan jama’armu kan yadda za a kirkiro da aikin yi. Wannan shi ne babban kalubale da ke gabanmu a kasar nan baya ga bambancin siyasa. Domin babbu yadda za ka iya kawar da bambancin siyasa saboda bambacin da ake tsakanin al’ummomin kasar nan.
Aminiya: Idan Allah Ya kai mu shekara ta 2015, kuma Ya sa jama’ar kasar nan suka fito suka ce sun sha wuya don haka ka zo ka cece su, za ka amince?
Allah kadai ke cetar mutane a dai ci gaba da rokon Allah Ya yi mana zabin da ya fi zama alheri.
Aminiya: Noma shi ne ginshikin tattalin arziki a kasar nan tun zamanin Turawa zuwa ’yancin kai, amma a yanzu noma ya zama cima-baya, sabanin yadda ake ta furucin a gwamnatance cewa za a inganta noma. Me za ka ce a matsayinka na tsohon manomi?
Batun gaskiya a nan ne ma al’amura suka fi lalacewa. Shekara 25 lokacin ina kungiyar ci gaban kasuwanci a matsayin maitaimakin shugaba na kasa muna ta ba su shawarwarin cewa a ba sashin noma aaalla kashi 25 cikin 100 na kasafin kudin Gwamnatin Tarayya.
Su ma gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi su yi haka, bankunan ba da bashi su ma su yi haka. Ni na tabbatar wa mutane inda na fito masu da jadawali a lokacin da nake neman shugabancin kasar nan cewa idan an yi haka sashin noma zai ba kasar nan ci gaban da man fetur ba zai ba ta ba. Kuma na fito da jadawali na nuna wa jama’a yadda abubuwan suke.
Yanzu ka shuka masara ko dawa da wake a fili kilomita 200 ka yi irin wannan kamar hudu a kasar nan tunda muna da fadin kasa. Abin da za a samu na kudi ya fi na man fetur. Kuma duk da fetur ne kan gaba a yanzu, amma duk da haka noma ke ba da kusan kashi 40 zuwa 47 na tattalin arzikin kasar nan.
Sannan jama’a kuma da suke amfana da noma sun kai kashi 70 a kasar nan. Nan ya kamata a dukufa a tada wannan sashi na noma domin mu ci da kanmu wanda kuma ya rage sai mu rika kaiwa kasashen waje muna sayarwa.
Aminiya: Mafi yawan kayan da ake amfani da su a kasar nan a fannin noma kusan ana shigowa da su ne daga kasashen waje, kana ganin idan za a inganta harkar noma za a iya cin moriyar al’amarin cikin kankanen lokaci?
Ba a cikin kankaen lokaci ba, amma na tabbata cikin shekara 15 zuwa 20 za a ci moriyar abin. Ba rana daya ake abubuwa ba, dole sai an sanya jari sannan a ci moriyar abin. Cikin wadannan shekaru in Allah Ya yarda za a cimma burin abin da nake fada maka.