’Yan Najeriya na dawowa daga gudun hijira
Tun fil-azal mutane na yin kaura a bisa dalilai daban-daban, duk da cewa an fi fita fafutuka don neman ilimi da fatauci, neman karfin iko wanda ya hada da yaki, hijira don samun mafaka a siyasance, neman lafiya duk inda take! Sannan akan yi kaura don nishadi.A zamanance kowa yana da kasar da ya fito […]
Tun fil-azal mutane na yin kaura a bisa dalilai daban-daban, duk da cewa an fi fita fafutuka don neman ilimi da fatauci, neman karfin iko wanda ya hada da yaki, hijira don samun mafaka a siyasance, neman lafiya duk inda take! Sannan akan yi kaura don nishadi.
A zamanance kowa yana da kasar da ya fito domin ba wanda ya sauko daga sama, ko aka tono shi daga kasa! A haka mutum kan zama dan kasa ta hanyar haihuwa, aure, rajista, zama a kasar ko karramawa. Akan yi kaura daga kauye zuwa kauye, yayin da kauran da ta fi shahara ita ce daga kauyuka zuwa birane, sannan ana kaura daga birni zuwa birni, ko daga birni zuwa kauye, wasu kan koma kauyuka don noma haka da bazara a shigo birane don kwadago ko a lokutan bukukuwa kamar kirismati ko sallah.
A yayin da tattalin arziki ya tabarbare ga ilimin ma ga ya nan yadda yake, dole wasu suke barin kasar don su tsira daga halin lahaula. Yayin da haka ba saba doka bane, sai dai gogan dan Najeriya, duk inda ya je sai an san ya zo, musamman domin sai ya bata wurin, tun ana marmarinsa za a fara korarsa, kuma ya makale!
Maza na da fahimtar fita da kansu don su yi ayyukan da zasu tsira da mutuncinsu, yayin da ko a cikin gida wasu kan yi kwadago kamar gini, dako inda ake tafiya ci-rani manyan birane ko Kudancin kasar nan.
kasashen waje, inda matasa ke da burin tarewa Turai har ake kasadar ratsa hamadar duk da hadarin da ake fuskanta, tare da wulakancin da mutum zai iske idan ma ya tsallaka! Baki ‘yan Najeriya kan yi bara, da wasu ayyuka kamar aikin karfi da ya hada da dako ko gini da wanke-wanke a gidajen abinci ko aiki a gidajen giya ko aiki a wurin ajiye gawa.
Akwai kasashe da dama da ba su da arzikin da Allah ya yiwa Najeriya, amma sun yi wa Najeriya fintinkau! Ta kowace fuska, yayin da ‘yan siyasa sun hallaka tattalin arzikin kasar, maimakon su gina kasar akan turbar ci gaban masana’antu da kimiyya da fasaha, sun gwammace su sace kudin kasar su kai waje. Don haka ‘yan kasa marasa gata ke zuwa Saudiyya su yi zaman shahada a kasa mai tsarki duk da tsarin dokokin da irin wulakanci da muzgunawar da suke fuskanta.
Rashin bin ka’idojin kasashen ketare, ya sa ake kama ‘yan Afrika musamman ‘yan Najeriya da hannun a barna a irin wadancan kasashen, su ne fashi da makami da fataucin miyagun kwayoyi ko fataucin mata da yara wasu su kafe da suna da mata hudu don su shigo da wadanda za su mayar kamar bayi, kafin su maida abin da suka kashe wajen shigo da matan bakuwar kasar.
Bincike ya nuna muhimmancin sanin wani a kasar ko samun wasikar gayyata, tabbatar da kudin da mutum zai rike kafin ya shigo kasar, sai ido a can! Idan kuma mutum ya gudu akan hukunta wanda ya tsaya masaa.
A farkon karnin da ya gabata Turawa sun yi galabar mallakar duniya, inda suka karkasa ta zuwa kasashe, wanda a da duk Musulmin da ya je Saudiyya ya je gida! Yayin da ko a yau akwai masana da malamai masu irin wannan ra’ayin na cewa zama dan Saudiyya Kalmar shahada, ta yadda da zarar mutum ya yi imani ya zama dan kasar!
Manyan mutane a kasashen waje ba su so a ce su ‘yan Najeriya ne, sannan gwamnati ta yi kunnen uwar shegu da irin wulakancin da ake wa ‘ya’yanta da uwar gaskiya ce ko ‘ya’yan sun yi laifi za ta kare tare da ba su tarbiyyar da ta kamata. Duk da albarkar da Allah ya yi wa Najeriya sai ya jarrabe ta da azzaluman shugabanni! Shi ya sa talakawa suke gudun hijira, tare da zama bakin haure, a wasu kasashe, domin halin da suka tsinci kansu na talauci da jahilci, musamman a tsarin jari-hujjanci da ke kadawa, amma Insha Allahu wahalar ta kusan zuwa karshe!
Gwamnati za ta iya daukar matakai; A ilimantar ta hanyoyin kafofin yada labarai. A fadakar ta hanyar ‘yan wasan kwaikwayo su yi fim da zai nuna illolin bakin haure da irin sharrin da suke jawo wa kasarsu ta haihuwa
Buhari Daure Muryar Talaka +2347035986444 [email protected].