’Yan Najeriya na kashe Naira tiriliyan daya da rabi don neman ilimi a waje – Rahoto

Wani rahoto da kungiyar tabbatar da adalci ta fitar. ya nuna cewa ’yan boko a Najeriya suna kashe kimanin Naira tiriliyan daya da rabi wajen tura ’ya’yansu manyan makarantu a kasashen ketare. A rahoton da kungiyar ta fitar mai lakabin: “Rahoto kan dokar da hukumar sanya idanu kan kudin da ma’aikatun gwamnati suke kashewa na […]

’Yan Najeriya na kashe Naira tiriliyan daya da rabi don neman ilimi a waje – Rahoto
’Yan Najeriya na kashe Naira tiriliyan daya da rabi don neman ilimi a waje – Rahoto

Wani rahoto da kungiyar tabbatar da adalci ta fitar. ya nuna cewa ’yan boko a Najeriya suna kashe kimanin Naira tiriliyan daya da rabi wajen tura ’ya’yansu manyan makarantu a kasashen ketare.

A rahoton da kungiyar ta fitar mai lakabin: “Rahoto kan dokar da hukumar sanya idanu kan kudin da ma’aikatun gwamnati suke kashewa na karshen shekarar 2013” wanda Aminiya ta samu kwafinsa a Abuja a karshen makon jiya, ya yi kira ga gwamnati ta yi maganin matsalar.
Rahoton ya ce, ’ya’yan ’yan bokon Najeriya sun yi watsi da manyan makarantun kasar nan saboda rashin ilimi mai inganci a makarantun kuma bincike ya nuna cewa suna kashe kimanin Naira tiriliyan daya da rabi wajen tura ’ya’yansu makarantun da ke wasu kasashen duniya.
Saboda haka sai rahoton ya shawarci gwamnati ta kara yawan kudin da take kashewa don magance kalubalen da bangaren ilimi ke fuskanta. Har ila yau, kungiyar ta yi kira ga ’yan majalisa su sauke nauyin da aka dora musu na sanya ido kan kasafin kudin da aka ware wa manyan makarantu tare da bin dididdigin kudin shigar da suke samu.
To amma sai dai rahoton ya soki jami’o’in kasar nan da karbar kudi daga kungiyoyin dalibai tare kuma da neman kudi daga kamfanoni masu zaman kansu. “Babu shakka jami’o’i da yawa suna karbar kudi daga kungiyoyin dalibai da kamfanoni masu zaman kansu,” inji rahoton.
Rahoton ya ce muddin ’yan majalisar dokoki suka dauki matakan da suka dace na sanya ido a kan kudin shigar manyan makarantu, babu shakka zai taimaka matuka wajen magance kalubalen da suke fuskanta.
Daga bisani rahoton ya nuna cewa hatta Naira biliyan 100 da kungiyar Malaman Jami’o’i da Gwamnatin Tarayya suka yi alkawarin a ware don tunkarar kaubalen da makarantun suke fuskanta, ba a shigar da shi cikin kasafin kudin bara ba.
Ya ce kudin da aka ware wa manyan jami’o’i a kasafin kudin shekarar 2014 bai kai Naira biliyan 50 ba. Saboda haka rahoton ya nuna cewa kudin sun yi kadan idan aka yi la’akari da dimbin matsalolin da ke addabar manyan makarantun, wadanda suka hada da rashin littafai da kayan aiki.