’Yan Najeriya na mutuwa saboda manufofin Tinubu – Ɗan Bello

Matashin ya ce idan gwamnatin Najeriya ba ta jin daɗin abin da yake yi, ta kai shi ƙara kotu.

’Yan Najeriya na mutuwa saboda manufofin Tinubu – Ɗan Bello

Bello Galadanchi, wanda aka fi sani da Ɗan Bello, mai barkwanci a shafukan sada zumunta, ya ce ’yan Najeriya na fama da yunwa sakamakon manufofin tattalin arziƙin Shugaba Bola Tinubu ya ɓullo da su.

Ɗan Bello ya bayyana hakan ne, yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Daily Politics na gidan talabijin na Trust TV a ranar Talata.

Ya ƙalubalanci gwamnati mai ci, cewa su kai shi kari idan ba sa jin daɗin abin da yake yi.

Ya jaddada cewa ba shi da wata alaƙa da kowace jam’iyyar siyasa a Najeriya, kuma ba ya yi wa kowa aiki.

Bello ya ce, “Idan abin da nake yi ya dame su, hakan yana nufin yana taimaka wa mutane. Idan manufofinsu suna da kyau, mutane ba za su ji cewa abin da nake yi yana kawo sauyi ba. Amma abin da yake faruwa yana nuna cewa abubuwan da suke yi na haifar da matsaloli.

“Manufofin gwamnati suna sa mutane cikin yunwa. Mutane na mutuwa. Wasu ma suna cin ciyawa suna sha ruwan da ya lalace. Wasu suna zuwa gida-gida suna neman a ba su ci abincin da za su ci.

“Wannan ba annoba ba ce; manufofi ne da za a iya kauce musu. Shugabannin sun samar da waɗannan manufofi sannan suka yi kunnen uwar-shegu da abin da suka haifar.

“Yanzu suna fushi saboda muna magana kan waɗannan manufofi. Suna son mu yi shiru yayinbda mutane ke fama da wahala. Da gaske? Ina mutuncinmu yake? Me ya sa za mu yi shiru yayin da muka san cewar yadda abubuwa ke tafiya a sauran ƙasashe, inda mutane ba sa fama da yunwa?

“Suna fushi saboda suna tara biliyoyin Naira suna yin ayyukan shirme. Eh, ina son su ji haushi. Ina son su kai ni kotu, su yi duk abin da za su iya domin su sa mu yi shiru. Wannan yana nufin cewa aikinmu yana ƙara yin tasiri.”

Matashin mai barkwanci, ya kan yi amfani da kafofin sada zumunta wajen aike da saƙo cikin shaguɓe ga ‘yan siyasa da sauran al’umma.

Sai dai a ’yan kwanakin nan sunansa ya karaɗe kafafen sada zumunta, sakamakon wani bidiyon zargin badaƙalar kuɗaɗe da ya sa ki game da tsohon mataimakin ɗan gwamnan Kano a jami’yyar APC, Murtala Sule Garo.