’Yan Najeriya sai sun zuba ruwa a kasa sun sha idan kotu ta soke zaben Tinubu – PDP
PDP ta ce tana da kwarin gwiwa cewar kotun za ta yi mata adalci
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta ce da zarar kotun sauraron ƙararrakin zaben Shugaban Kasa ta soke nasarar Bola Tinubu, sai ’yan Najeriya sai sun mamaye titunan Najeriya don murna.
Daraktan Tsare-tsare na Kwamitin Yakin Neman Zaɓen Shugaban Kasa na jam’iyyar, Pedro Obaseki, ne ya bayyana hakan a Abuja.
- Idris Abdulaziz zai ci gaba da zama a kurkuku saboda gaza cika sharudan belinsa
- Tinubu ya bai wa Abdullahi Abbas muƙami
Obaseki, wanda ya yi wa manema labarai jawabi a harabar kotun, ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa PDP na da yaƙinin kotun za ta yi shari’a mai adalci da dukkanin jam’iyyun za su aminta da ita.
Ya kuma ce, duba da irin gamsassun hujjojin da suke da su, alƙalan kotun za su yi abin da ya dace.
Obaseki, wanda shi ma lauya ne, ya yi tsokaci akan karar da jam’iyyar APM da ke neman a soke zaben Tinubun, inda ya ƙara da cewa “dole a duba batun cancanta”
Jam’iyyar APM wacce ke kalubalantar nasarar Tinubu da INEC ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban Kasar da aka yi a watan Fabrairu, ta kafa hujja da cewa Shettima, ya haɗa takara biyu ta Sanata da ta Mataimakin Shugaban Kasa kafin ranar zaben.