’Yan Najeriya su daina fargabar zaben 2019 – Shugaban Cocin BCS
Shugaban Cocin BCS, Olumba-Olumba Obu ya bukaci ’yan Najeriya su kwantar da hankalinsu, su daina zullumi ko fargaba kan yadda zaben 2019 zai kasance, musamman yadda wadansu ke hasashen rikici ka iya barkewa a tsakanin magoya bayan ’yan takarar jam’iyyun APC da PDP da suka fito daga Arewa. Shugaban ya bayyana haka ne ga manema […]
Shugaban Cocin BCS, Olumba-Olumba Obu ya bukaci ’yan Najeriya su kwantar da hankalinsu, su daina zullumi ko fargaba kan yadda zaben 2019 zai kasance, musamman yadda wadansu ke hasashen rikici ka iya barkewa a tsakanin magoya bayan ’yan takarar jam’iyyun APC da PDP da suka fito daga Arewa.
Shugaban ya bayyana haka ne ga manema labarai a Kalaba domin murnar bikin cika shekara 100 da kafa majami’ar da kuma zagayowar ranar jinkai da tallafa wa marasa galihu da cocin yake yi kowane makon farko na watan Disamba.
Ya ce “Yadda wadansu ’yan Najeriya suka tsorata suke fargabar rikici ka iya barkewa a zabe, Allah Ya riga ya zabi bayinSa nagari masu tsoronSa da kuma son kamanta adalci. Don haka babu wani tashin hankali da za a samu a zabe mai zuwa, kowa ya kwantar da hankalinsa.”
Shugaban Cocin BCS din ya ce yana mamakin yadda wadansu ke neman shugabanci ko ta halin kaka alhalin ba su tsoron Allah ko da tunanin haduwarsu da shi a gobe Kiyama.
Olumba Obu ya alakanta kashe-kashen da ake yi da kama mutane ana garkuwa da su domin neman kudin fansa da cewa duk siyasa ce, kuma ya hore su da su ji tsoron Allah su daina zubar da jini haka.
Ya ce “Idan aka ba gwammati dama shekara hudu masu zuwa barnar da aka yi za ta gyaru, kowane dan kasar nan zai samu kwanciyar hankali da karuwar arziki.”