’Yan Najeriya sun fi wata 6 suna azumi kafin Ramadan — Alaramma Mujahid

Malamim ya ce ƙagin talauci da aka shiga ya sanya wasu daukar dabi’ar yin azumi kullum.

’Yan Najeriya sun fi wata 6 suna azumi kafin Ramadan — Alaramma Mujahid

Wani Malamin Addinin Islama a Jihar Gombe, Alaramma Mujahid Baure, ya bayyana cewar halin yunwa ya sanya ‘yan Najeriya daukar yin azumi kullum.

Malamin ya kuma gargadi shugabanni da ‘yan siyasa kan karbar shaida da bayanan karya daga hadiminsu, domina cewarsa jama’a na cikin halin tsanani a kasa nan.

Malamin ya bayyana hakan ne lokacin da yake gabatar da tafsirinsa, a masallacin Kofar Hakimin Kwadom da ke Karamar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe

Ya ce duk mai mulki ba lallai ne kunnensa ko idonsa ya kai ko ina ba dole sai an samu masu isar musu da koken al’umma.

Ya ce talaka yana cikin wahala domin watanni shida da suka gabata talaka ke azumi tun kafin zuwan Ramadan.

Sannan ya yi kira ga shugabanin da su ji tsoron Allah domin zai tambaye su halin da talakawa suke ciki.

Yau ita ce ranar ta hudu da al’ummar Musulmi suka fara azumin watan Ramadan a Najeriya.

Tun bayan sanarwar ganin watan Ramadan na bana, mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya bukaci mai hannu da shuni da ‘yan siyasa da su taimaki marasa karfi.