’Yan Najeriya sun gamsu da kamun ludayin Buhari – Maizabura

Wani tsohon dan siyasa kuma mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum a Jihar Borno Alhaji Umar Muhammad Maizabura ya bayyana salon mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mulki na adalci da sanin ya kamata.Alhaji Umar Maizabura, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Maiduguri, inda ya ce ko […]

’Yan Najeriya sun gamsu da kamun ludayin Buhari – Maizabura
’Yan Najeriya sun gamsu da kamun ludayin Buhari – Maizabura

Wani tsohon dan siyasa kuma mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum a Jihar Borno Alhaji Umar Muhammad Maizabura ya bayyana salon mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mulki na adalci da sanin ya kamata.
Alhaji Umar Maizabura, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Maiduguri, inda ya ce ko shakka babu kamun ludayin Shugaba Buhari abu ne da ya gamsar da akasarin al’ummar Najeriya, musamman yadda yake kokarin shawo kan matsalar tattalin arziki da gyara matatun man fetur da gwamnatin PDP ta kashe su.
Ya ce Shugaba Buhari ya kuma ya samar da daidaitaccen farashin man fetur a kasa baki daya da inganta samar da wutar lantarki da yaki da cin hanci da rashawa.
Alhaji Maizabura ya ce babbar nasarar da gwamnatin Buhari ta samu ita ce hanyoyin da take bi wajen magace matsalar tsaro da ta addabi Arewa maso Gabas “Mu talakawa mun gamsu da kamun ludayin Shugaba Buhari, kuma ya kamata ’yan adawa su goya masa baya saboda Shugaba Buhari ya dauko hanyar gyara kasar nan,” inji shi.
Maizabura ya shawarci Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kashim Shettima ya zakulo mataimaki mai
adalci da sanin ya kamata, kuma mai zafin nama da son jama’a, domin maye gurbin marigayi Zanna Umar wanda mutum ne mai son jama’a da kokari wajen aiki ga al’umma.
Sai ya roki al’ummar jihar su bai wa jami’an tsaro cikakken hadin kai da goyon baya don samun nasarar yaki da ta’addanci da suke yi a yanzu a sassan jihar.
Sheikh Kabir Gombe ya yaba wa kwamitin shirya wa’azi a karkashin shugabancin Alhaji Ahmed Shu’aibu Gara Gombe, inda ya ce akwai bukatar a rika gudanar da irin wanan taro bisa lura da halin da kasar nan take ciki.