’Yan Najeriya sun koma girki da gawayi da itace saboda tashin farashin gas
Mutane da dama sun koma amfani da gawayi ko itace domin nema wa kansu sauƙi.
Tashin farashin gas ɗin girki ya tilasta wa gidaje da dama a Najeriya daina amfani da shi, tare da komawa amfani da gawayi da itace wajen yin girki.
A sassa daban-daban na ƙasar, magidanta sun ce ba za su iya ci gaba da sayen iskar gas ɗin ba saboda yadda yake ci gaba da yin tsada.
- Mutanen da aka sace a cocin Kwara sun mutu a hannun ’yan bindiga
- Fitaccen ɗan kasuwar mai na Kano, Audu Manager, ya rasu
Ƙungiyar Dillalan Iskar Gas ta Najeriya (NALPGAM) ta yi gargaɗin cewa ci gaba da tashin farashin gas na iya haifar da rashin jin daɗi a tsakanin jama’a idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba.
Ƙungiyar ta ce dillalai na fuskantar matsaloli kamar tsadar shigo da kaya, kuɗin sufuri, da kuma ƙarancinsa, wanda ke ƙara ruruta tashin farashin.
NALPGAM, ta bayyana cewa waɗannan matsaloli sun sa sayar da gas ɗin ya fi tsada.
Hakan ya sa farashinsa ya tashi sosai, lamarin da ke matuƙar wahala ga mutane da ƙananan ’yan kasuwa da ke dogaro da shi wajen girki.
Matsalolin da jama’a ke fuskanta a jihohi daban-daban
A jihohi da dama kamar Kaduna, Kano, Gombe, Ribas, Borno, Filato da Legas, jama’a sun ce sun fara nema wa kansu mafita wajen yin girki.
Yawancin gidaje yanzu suna amfani da gas ne kawai wajen abubuwa kaɗan kamar tafasa ruwa, yayin da suke amfani da gawayi ko itace wajen dafa abinci.
A Kaduna, mazauna jihar sun ce gawayi yana da arha. Wasu sun bayyana cewa suna sayen gas ne kawai idan sun samu kuɗi, amma yawanci sun fi dogara da gawayi saboda arha da kuma daɗewar da yake yi.
A Kano kuwa, gidaje da yawa sun daina amfani da gas gaba ɗaya saboda tashin farashinsa zuwa tsakanin Naira 1,500 zuwa Naira 1,550 kan kowane kilo.
Kanawa sun ce yanzu suna amfani da gawayi da itace duk da wahalar da hakan ke haifarwa.
A jihohin Ribas da Bayelsa, mutane da dama sun koma amfani da gawayi. Sun ce itacen girki ya fi arha, ko da yake yana fitar da hayaƙi kuma ba shi da sauƙin amfani kamar gas.
A Legas kuma, wasu mazauna jihar suna amfani da sabbin hanyoyin girki kamar amfani da murhu na lantarki da sauransu.
Sai dai sun ce ba a ko’ina ake samun sa ba kuma ba su maye gurbin gas gaba ɗaya ba.
Illar da ke tattare da hakan ga lafiya da muhalli
Masana harkar makamashi sun yi gargaɗin cewa komawa amfani da gawayi da itace wajen yin girki na iya haifar da matsalolin lafiya da muhalli masu tsanani.
Sun ce hayaƙin da ke fitowa daga waɗannan hanyoyi na iya haddasa cututtukan numfashi, musamman ga mata da ƙananan yara.
Sun kau ƙara da cewa ƙaruwar amfani da itace na iya ƙara yawan sare dazuzzuka da lalata muhalli, wanda zai ƙara dagula matsalar sauyin yanayi.
Bugu da ƙari, sun ce talakawa da masu matsakaicin ƙarfi su ne suka fi shan wahala, domin suna kashe kaso mai yawa na kuɗin da suke samu wajen girki ko kuma su koma hanyoyin da ba su da sauƙi da lafiya.
Kiran da masu ruwa da tsaki suka yi
Masu ruwa da tsaki sun yi kira ga gwamani da ta ɗauki mataki wajen daidaita farashin gas da inganta hanyoyin samar da shi.
Haka kuma sun buƙaci a zuba jari a makamashi mai tsafta kuma mai sauƙi ga jama’a.
A halin yanzu kuwa, yawancin ’yan Najeriya na ci gaba da daidaita rayuwarsu da tsadar rayuwa, suna komawa tsoffin hanyoyin girki domin su samu sauƙin al’amuran ta yau da kullum.