‘Yan Najeriya sun kosa PDP ta dawo- David Mark
Tsohon shugaban Majalisar Dattijai, David Mark ya ce ‘yan Najeriya sun kosa su ga Jam’iyyar PDP ta karbi karagar mulkin kasar nan a wajen APC. David Mark ya yi wannan furucin ne a lokacin da yake karban bakuntan Chief Raymond Dokpesi, wanda ya kawo masa ziyara domin neman goyon bayansa a fafutukar da yake yi […]

Tsohon shugaban Majalisar Dattijai, David Mark ya ce ‘yan Najeriya sun kosa su ga Jam’iyyar PDP ta karbi karagar mulkin kasar nan a wajen APC.
David Mark ya yi wannan furucin ne a lokacin da yake karban bakuntan Chief Raymond Dokpesi, wanda ya kawo masa ziyara domin neman goyon bayansa a fafutukar da yake yi na zama shugaban Jam’iyyar PDP a babban taron ta da ke tafe, a watan gobe.
Hakanan kuma David Mark ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar da kada su yi magudi wajen zaban sabon shugaban jam’iyyar, inda ya ce su dubi zaben 2015 a matsayin darasi.
“’Yan Najeriya sun kosa su ga PDP ta dawo kan karagar mulki, don haka kada mu watsa musu kasa a fuska. Muna bukatar shugaban jam’iyya mai nagarta da mutuncin da zai iya jagorantar jam’iyyar zuwa ga gaci a zaben 2019,” inji Mark, ta hannun mataimakinsa wajen yada labarai, Paul Mumeh.
Kafin nan, sai da Chief Raymond Dokpesi ya shaida wa David Mark cewa yana neman zama shugaban jam’iyyar ne saboda ya san cewa ya cancanta, kuma zai iya kai jam’iyyar ga samun nasara.