’Yan Najeriya sun kusa yin farin ciki — Remi Tinubu
Ta buƙaci ‘yan ƙasar su kasance masu yin fata na gari.
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga ’yan Najeriya su kasance masu yi wa ƙasar kyakkyawan fata, domin lokacin farin ciki yana daf da zuwa.
A saƙonta na Kirsimeti, ta nuna godiyarta ga ‘yan Najeriya saboda goyon baya da haƙurin da suka nuna yayin da mijinta ke ƙoƙarin inganta ƙasar.
- Mutum 3 sun mutu yayin da tanka ta murƙushe adaidaita sahu a Jos
- Ban yi nadamar cire tallafin man fetur ba – Tinubu
Ta ce, “A ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, mun duƙufa wajen aiwatar da gyare-gyare da za su amfanar da kowa.
“Kuma da dama daga cikin matakan da muka ɗauka sun fara samar da sakamako mai kyau.
“Yayin da muke kammala wannan shekara, mu ci gaba da kasancewa masu kyakkyawan fata da yaƙinin cewa lokacin farin ciki na tafe.
“Mu ci gaba da ƙaunar juna, tallafa wa juna, da kuma ƙarfafa haɗin kai tare da yabawa bambance-bambancen da suka sa ƙasarmu ta zama mai ƙarfi.
“Ina yi muku fatan alheri a bikin Kirsimeti da kuma murnar shigowar shekarar 2025 mai albarka, cike da soyayya, farin ciki, zaman lafiya, da ci gaba,” in ji ta.