’Yan Najeriya sun yi bikin ’yancin kasarsu a birnin New York

Dubban ’yan Najeriya daga sassa da dama na kasar Amurka da kewaye sun taru a birnin New York don yin shagulgulan tunawa da ranar samun ’yancin kai na kasarsu. Wakilin kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa bikin wanda shi ne mafi girma da ’yan Najeriya suke yi a wajen kasar su an shirya […]

’Yan Najeriya sun yi bikin ’yancin kasarsu a birnin New York

Dubban ’yan Najeriya daga sassa da dama na kasar Amurka da kewaye sun taru a birnin New York don yin shagulgulan tunawa da ranar samun ’yancin kai na kasarsu.
Wakilin kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa bikin wanda shi ne mafi girma da ’yan Najeriya suke yi a wajen kasar su an shirya shi ne don yin murnar cikar Najeriya shekaru 57 da samun ’yancin kai daga turawan mulkin mallaka.
Daga cikin kungiyoyin ’yan Najeriyan da suka shiga bikin sun hada da kungiyar ’yan kabilar Igbo da kungiyoyin ’yan Najeriya da ke kasar Amurka da kungiyoyin addini da kungiyar ungozoma ta Amurka da kungiyar bunkasa al’adun Najeriya.