’Yan Najeriya suna zukar karan taba biliyan 20 duk shekara – Minista
Gwamnatin Tarayya ta nuna damuwa kan hauhawar zukar taba sigari a kasar nan, inda ta ce kimanin ’yan Najeriya miliyan hudu da rabi suna zukar karan taba biliyan a kowace shekara. Ministan Lafiya Farfesa Isaac Adewole ya bayyana haka a ranar Litinin da ta gabata a wurin wani taron fadakarwa da aka shirya wa hukumomin […]

Gwamnatin Tarayya ta nuna damuwa kan hauhawar zukar taba sigari a kasar nan, inda ta ce kimanin ’yan Najeriya miliyan hudu da rabi suna zukar karan taba biliyan a kowace shekara.
Ministan Lafiya Farfesa Isaac Adewole ya bayyana haka a ranar Litinin da ta gabata a wurin wani taron fadakarwa da aka shirya wa hukumomin tsaro da kafafen watsa labarai kan aiwatar da Dokar Takaita Shan Taba ta Shekarar 2015 a Abuja.
Ministan ya ce matakan rigakafi da gwamnati ke dauka ta hanyar dokar takaita shan taba za su kunshi haramta shan taba ga matasan da ba su kai shekara 18 ba, da kuma hana shan taba a tashoshin mota da kasuwanni da gidajen cin abinci da sauran wuraren taruwar jama’a.
Farfesa Adewole, wanda Shugabar Sashin Kula da Lafiyar Jama’a ta Ma’aikatar Dokta Ebelyn Ngige, ta karanta jawabinsa ya ce, “Binciken da aka gudanar game da baligan mutane da suke zukar taba ya nuna fiye da karan taba sigari biliyan 20, baligai miliyan hudu da rabi ke sha a kasar nan. Wannan kashi 5 da digo 6 na jama’ar kasarmu ken an. Kuma binciken ya nuna maza miliyan hudu da dubu 100 da mata dubu 500 ne ke shan taba a Najeriya, yayin baligai miliyan 6 da digo 4 suke fuskantar illar mashaya sigarin. Kuma wajibi ne mu yaki wannan annoba yanzu.”
Ministan ya kara da cewa: “A watan Mayun bana, Hukumar Lafiya ta Duniya ta ba da rahotin cewa taba tana kashe fiye da mutum miliyan bakwai duk shekara. Kuma mutum miliyan shida suna mutuwa ne saboda zukar tabar kai-tsaye, yayin da sauran suke mutuwa saboda shakar hayakin tabar daga masu shanta. Masu karancin samu da matsakaitan masu samu a kasashe irin Najeriya ne kashi 80 cikin 100 na masu fama da cututtukar shan taba sigari ko ma take hallaka su. Wannan yana kara tabarbarar da harkokin kiwon lafiyarmu wanda dama ba mai karfi ba ne.”
Ministan ya yi kira ga hukumomin tsaro ciki hard a Hukumar Kwastam ta Najeriya su fito da tsauraran ka’idoji a kan kamfanonin taba da masu sayar da ita ta yadda za a raunana al’adar shan tabar.
“Taba ita ce kadai aka fi jingina tad a nau’o’in cutar daji (kansa). Kuma tana bayar da gudunmawa ga tabarbarewar lafiyar jama’a. Kuma gwamnati za ta fara haramta sayar da taba ga duk wanda bai kai shekara 18 ba. Na biyu za a takaita sayar da taba a fakiti mai dauke da kara 20. Kuma za mu hana sayar da taba ta kafafen sadarwa da sauran hanyoyin sadarwa na zamani. Kuma za a haramta sha ko sayar da taba a harabobin kula da yara da cibiyoyin ilimi da na kiwon lafiya,” inji Ministan.