`Yan Najeriya zasu samu walwala a mulkin PDP – Obi
Mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Mista Peter Obi, ya ce, jam`iyyar zata sanya ‘yan Najeriya annashuwa da walwala idan suka lashe zaben takarar shugaban kasa da za a yi ranar 16 ga Fabirairu 2019. Obi ya bayyanawa manema labarai hakan ne a jiya Talata a wani taron siyasa da aka yi a […]
Mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Mista Peter Obi, ya ce, jam`iyyar zata sanya ‘yan Najeriya annashuwa da walwala idan suka lashe zaben takarar shugaban kasa da za a yi ranar 16 ga Fabirairu 2019.
Obi ya bayyanawa manema labarai hakan ne a jiya Talata a wani taron siyasa da aka yi a Awka babban birnin jihar Anambra.
Obi ya kara da cewa, jam’iyyar PDP zata farfado da tattalin arzikin Najeriya da mulkin APC ta durkusar, kuma ci gaba da zaben APC a karo na biyu za a sake raunata kasar.