‘Yan Neja dalta sun nemi a zauna lafiya

Wata kungiya mai suna Peace in Niger Delta ta daura damarar ganin yankin ya ci gaba da zaunawa  lafiya ba tare da wani tashin hankali ko ta’addanci ba. kungiyar wadda ta gudanar da taronta na shiyya a Kalaba jahar Kurosriba, ta bayyana cewa babu wani yanki ko kasa, da za ta ci gaba matukar babu […]

‘Yan Neja dalta sun nemi a zauna lafiya
‘Yan Neja dalta sun nemi a zauna lafiya

Wata kungiya mai suna Peace in Niger Delta ta daura damarar ganin yankin ya ci gaba da zaunawa  lafiya ba tare da wani tashin hankali ko ta’addanci ba.
kungiyar wadda ta gudanar da taronta na shiyya a Kalaba jahar Kurosriba, ta bayyana cewa babu wani yanki ko kasa, da za ta ci gaba matukar babu zaman lafiya.
Wakinlin kungiyar na shiyyar kudu maso kudu Godwin Ebele shi ne ya bayyanawa Aminiya haka bayan da suka kammala taron shiyyyar da sukayi a kalaba babban birnin jahar kuros riba.
“Sai da zaman lafiya ne ake samun kwanciyar hankali da karuwar arziki idan babu zaman lafiya babu yadda za ayi al’umma su yi barci ballantana ma har mu fita neman abunci da muka saba na yauda kullum. Wannan daliline ya sanya muke karade tun daga kan matakin anguwanni zuwa birane, da kauyuka da sauran garuruka na wann shiyya domin fadakar da al’umma”.
Alhaji Shaaban Abdullahi jigo a kungiyar reshen kuros riba tsokacin da ya yi game da ayyuka da kuma nasarorin da kungiyar tasu ta samu, “gamsuwa da kokarin da kungiyar takeyi  na san zaman lafiya ya ci gaba da wanzuwa a jahohin kudu maso kudu ne ya sanya na yarda na amince in zama dan kungiyar. Saboda gaskiya babu abinda yafi zaman lafiya.”