’Yan Nijar sun fi mu jin haushin cire tallafin mai – Akpabio

Ya ce tuni suka fara zanga-zanga a kan haka

’Yan Nijar sun fi mu jin haushin cire tallafin mai – Akpabio

Godswill Akpabio, Ministan Neja Delta

Daya daga cikin na gaba-gaba a masu neman Shugabancin Majalisar Dattijai ta 10, Godswill Akpabio, ya ce mutanen makwabtan kasashe sun ma fi ’yan Najeriya jin haushin cire tallafin man fetur din da aka yi.

Ya kuma ce rahotanni sun nuna tuni wasu daga cikinsu ma sun fara zanga-zanga a kasashe irin su Nijar da Kamaru kuma Jamhuriyar Benin.

Akpabio, wanda kuma tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom ne ya bayyana hakan ne ranar Litinin, lokacin da Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya duba faretin da aka shirya masa a Fadar Aso Rock da ke Abuje.

An shirya bikin ne a wani bangare na bikin Ranar Dimokuradiyya ta bana.

A cewar Akpabio, hatta alkaluma sun nuna an samu raguwa matuka a yawan man da ake sha a kullum a fadin Najeriya tun bayan cire tallafin, inda ya ce za a yi amfani da rarar kudin wajen inganta rayuwar ’yan Najeriya.

Ya ce, “Za mu rika shan man da muke tacewa, kuma za mu rika tace man da zamu sha, kuma na tabbatar da wadannan kudaden na tallafi da suka zame mana karfen kafa, za a gyara matatun manmu su dawo aiki yadda ya kamata.

“Ban san nawa ne alkaluman ba, amma wani ya ce min kusan ganga 9ko kuma lita) miliyan 69 muke sha a kullum kafin a cire tallafi, amma yanzu ya dawo miliyan 15.

“Wannan ne ma ya sa makwabtan kasashe suke zanga-zanga, saboda kusan dukkan kasashe makwabtanmu na Yammacin Afirka muke biya wa tallafin,” in ji shi.

A ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata ce dai Shugaba Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur din gaba daya yayin jawabinsa na rantsuwa.

Tsofaffin ma’aikatan Gombe 2,204 sun karɓi giratuti N4.2bn

Bam ya yi ajalin ɗaliban Islamiyya 2 a Abuja 

Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Saudiyya

’Yan sanda sun ceto yara 4 da aka sace daga Bauchi a Anambra