‘Yan Nijeriya miliyan 32 za su fuskanci matsananciyar yunwa — IRC
Matsalar karancin cimakar za ta fi kamari a jihohin Arewacin Najeriya irinsu Sakkwato da Zamfara.
Akwai yiyuwar akalla ‘yan Najeriya miliyan 32 za su fuskanci wani yanayi mai kama da matsananciyar yunwa a tsakanin watanin Yuni da Agustan bana matuƙar ba a ɗauki matakan gaggawa ba.
Wannan na ƙunshe cikin rahoton ‘Cadre Harminise’ na baya-bayan nan, wanda Kwamitin Kai Ɗauki na Ƙasa da Ƙasa IRC da gomman kungiyoyin kasa da ke aiki a yankin suka wallafa.
- An kashe makiyaya 2 da shanu 150 a sabon hari a Filato
- ‘Yan bindiga sun sace ɗalibai 9 a Jami’ar Kogi
A cewar rahoton na IRC, adadin mutanen da za su fuskanci matsalar ƙarancin abinci a yankunan yammaci da tsakiyar nahiyar Afirka a wannan dan tsakani zai kai kimanin mutane miliyan 52 kwatankwacin kaso 12 cikin 100 na mutanen da aka tantance.
Rahoton ya bayyana cewar, “a bisa tsinkayen da muka yi, abin da ake hasashen zai faru tsakanin watannin Yuni zuwa Agustan shekarar da muke ciki zai ma fi yadda ake tunani tsanani.
“Ana sa ran kimanin mutane milyan 52 daga kasashe 17 da aka nazarta za su fuskanci gaba ta 3 zuwa ta 5 na wannan lokaci na karancin cimaka tsakanin watan Yuni zuwa Agusta.
“Hakan na nufin cewar kaso 12 cikin 100 na al’ummar da aka nazarta za su sha bakar wahala wajen samun abin kaiwa bakin salatinsu.
Kasashen da al’amarin zai shafa sun hadar da Mauritaniya (inda zai shafi mutane 656, 652, kwatankwacin kaso 14 cikin 100) da Burkina Faso (inda zai shafi mutane 2, 734, 196, kwatankwacin kaso 12 cikin 100) da Nijar (inda zai shafi mutane 3, 436, 892, kwatankwacin kaso 13 cikin 100) da Chadi (inda zai shafi mutane 3, 364, 453, kwatankwacin kaso 20 cikin 100) da Saliyo (inda zai shafi mutane 1, 569, 895, kwatankwacin kaso 20 cikin 100) da Najeriya (inda zai shafi mutane 31, 758, 164, kwatankwacin kaso 16 cikin 100).
Har ila yau, rahoton ya kara da cewar matsalar karancin cimakar za ta fi kamari a jihohin Arewacin Najeriya irinsu Sakkwato da Zamfara inda fashin bakin da aka yi ya bayyana yanayin da mai matukar tsanani, har ma fiye da kaso 15 cikin 100 na kananan yara za su yi fama da cutar tamowa da karancin abinci ke haddasawa.
Rahoton na IRC ya alakanta dalilan tsanantar matsalar karancin cimakar a yankin sahel ga matsalolin rashin tsaro da sauyin yanayi da kuma tabarbarewar tattalin arzikin kasashe, musamma ma matsalar hauhawar farashin kayan masarufi.
A watan Janairun da ya gabata, yawaitar hauhawar farashin kayan masarufi ta kai kaso 21 cikin 100, inda ya karu daga kaso 18 cikin 100 da aka gani a shekarar bara.
Kasashen da al’amarin ya fi kamari ma sune irinsu Saliyo inda hauhawar farashin ta kai har kaso 54 cikin 100.