‘Yan Nijeriya miliyan 33 na iya fuskantar ƙarancin abinci a shekarar 2025 – Rahoto

Daga cikinsu, miliyan 3.8 na zaune a jihohin Arewa maso Gabas – adadin da aka yi hasashen zai haura miliyan 5 nan da shekara ta 2025.

‘Yan Nijeriya miliyan 33 na iya fuskantar ƙarancin abinci a shekarar 2025 – Rahoto

Matsalar ƙarancin abinci a Nijeriya za ta ƙara taɓarɓarewa nan da shekarar 2025 kuma za ta iya jefa ‘yan Nijeriya sama da miliyan 33 cikin yunwa.  

Ƙidayar al’ummar ƙasar a halin yanzu yana kusan miliyan 223.8.

Wani rahoto na Cadre Harmonisé da gwamnatin tarayya ke jagoranta tare da goyon bayan abokan hulda, ciki har da hukumar samar da abinci ta Majalisar Ɗ inkin Duniya, ta yi gargaɗ in taɓarɓarewar samar da abinci a Nijeriya, inda aka yi hasashen mutane miliyan 33.1 za su fuskanci matsanancin ƙarancin abinci a lokacin bazara mai zuwa tsakanin watannin Yuni zuwa Agusta 2025.

Bincike ya nuna cewa mutane miliyan 33.1 sun nuna ƙaruwar mutane miliyan bakwai idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.

Hasashen ya samo asali ne sakamakon matsalolin tattalin arziki da ake fama da su a halin yanzu, hauhawar farashin kayayyaki da tasirin sauyin yanayi da kuma tashe-tashen hankulan da ya addabi a jihohin Arewa maso Gabas.

A cewar rahoton, tsakanin Oktoba da Disamba 2024, kusan mutane miliyan 25.1 na iya fuskantar ƙarancin abinci, har zuwa tsakiyar lokacin girbin amfanin gona.

Daga cikinsu, miliyan 3.8 na zaune a jihohin Arewa maso Gabas – adadin da aka yi hasashen zai haura miliyan 5 nan da shekara ta 2025.