’Yan Nijeriya su ƙara haƙuri kan matakan da muke ɗauka — Tinubu
Matata kirista ce, don haka ba zan zama wanda zai bari a yi wa kiristoci kisan mummuƙe ba.

Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci ’yan Nijeriya da su ƙara haƙuri kan matakan da gwamnatinsa ke ɗauka domin kawo ci gaba a ƙasar.
Tinubu ya ce duk da cewa gwamnatinsa mai sauraron koken jama’a ce, amma yana so a ƙara haƙuri domin akwai haske nan gaba.
- Minista ya caccaki El-Rufai kan sukar Tinubu da APC
- Sojoji sun hallaka shugabannin ’yan bindiga 2 da wasu a Katsina
Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, ta ruwaito Tinubu yana wannan furuci ne a ranar Juma’a, yayin da ya karɓi baƙuncin ƙungiyar fastocin Cocin Katolika ta Catholic Bishop’s Conference of Nigeria (CBCN) a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Ya bayyana wa malaman cocin cewa ya ɗauki matakai masu tsauri bayan ya karɓi mulki a shekarar 2023, ciki har da cire tallafin man fetur.
“Lallai cire tallafin man fetur mataki ne mai tsauri, amma ya zama dole ne domin ba za mu ci gaba da jinginar da ƙasarmu ba,” in ji shi.
“Sai dai akwai alamun nasara da sauƙi a gaba. Ana bayyana abubuwa masu kyau game da Nijeriya, kuma ina alfahari da haka. Matakan nan masu tsauri yanzu sun fara nuna alamomi masu kyau.”
Ya ce damina ta yi albarka wanda hakan ya sa farashin kayan abinci yake sauka, sannan farashin man fetur ma yana sauka.
A game da batun hare-haren ta’addanci, Tinubu ya ce rashin tsaro yana shafar musulmi da kirista, inda ya ƙara da cewa matarsa kirista ce, don haka ba zai zama mai yi musu kisan mummuƙe ba.