’Yan Nijeriya za su ci moriyar sauye-sauyen haraji da muka kawo — Shettima

Gwamnatin Shugaba Tinubu ba ta da burin tsawwalawa ’yan Nijeriya.

’Yan Nijeriya za su ci moriyar sauye-sauyen haraji da muka kawo — Shettima

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya ce sauye-sauyen harajin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke kawowa suna da nufin inganta tsarin kasar ne ta yadda duk ’yan Nijeriya za su amfana baki daya.

Shettima ya faɗi hakan ne ranar Asabar yayin wani taro da kwamitin shugaban kasa ya kafa kan tsare-tsaren kuɗi da haraji ya gudanar a Otel din Transcorp Hilton da ke Abuja.

Mataimakin Shugaban Kasar ya ce sabanin yadda ake yada jita-jita, gwamnati ta kudiri niyyar “kirkirar tsarin gwamnati da zai tabbatar da cin moriyar tsarin harajin da dukkan ‘yan kasa za su amfana.”

Kashim wanda ya samu wakilcin mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan ayyuka, Dokta Aliyu Modibbo Umar, ya ce gwamnati ba ta da burin tsawwala wa ’yan Nijeriya.

“Burinmu shi ne sake farfado da tsarin haraji a Najeriya yayin da muke neman abokan hulɗa da za su sanya hannun jari mai ɗorewa kuma kasarmu ta zama wadda ake gogawa da ita da fuskar kasuwanci a duniya baki daya.

“Ina da yakinin cewa gwamnatin tarayya da ta jihohi a shirye suke don tabbatar da aiwatar da shawarwarin da aka gabatar na aiwatar da gyara yadda ya kamata.

“Kuma za mu samar da tsare-tsaren hukumomin da za su ba da tabbacin amincewa da shawarwarin wannan kwamiti, tare da daidaita su da manufofin tattalin arzikinmu,” in ji shi.