’Yan PDP 4,400 sun sauya sheka zuwa APC a Binuwai
Mambobin Jam’iyyar adawa ta PDP kimanin 4,450 sun sauya sheka zuwa APC mai mulki a Jihar Binuwai.
Mambobin Jam’iyyar adawa ta PDP kimanin 4,450 sun sauya sheka zuwa APC mai mulki a Jihar Binuwai.
Masu sauya shekar da suka fito ne daga kananan hukumomin Katsina-Ala, Ukum, Logo, Kwande da kuma Ushongo sun koma APC ne a ranar Talata.
Gwamnan jihar, Hyacinth Alia, ne ya karbe su a wani biki a yayin da yake gudanar da rangadin godiya ga al’ummar jihar.
Gwamnan yana yin zagaye a daukacin kananan hukumomin jihar ne domin nuna godiyarsa bisa goyon bayan da ya samu har ya lashe zaben 2023.
- Tirela ta makarɗe mutum 2 har lahira a titin Abuja-Keffi
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 6, sun ƙone gidaje a Kaduna
A jawabinsa a wurin karbar masu sauya shekar, Gwamnan Alia ya bayyana godiyarsa kan goyon bayan da ya samu a matsayin sabon shiga siyasa, amma ya kayar da sauran masu neman kujerar.
Daga nan ya jaddada shirinsa na sake mayar da al’ummomin da hare-haren ’yan bindiga suka raba da gidajensu zuwa yankunansu domin ci gaba da harkokinsu yadda suka saba a baya.
Da yake nuna damuwa bisa yadda hare-haren suka addabi yankin Sankera, cibiyar noman doya a jihar, Gwamna Alia ya jaddada cewa aniyarsa ta samar da tsaro a jihar.