’Yan PDP ne suka murguda maganar Buhari kan matasan Najeriya – danladi Pasali

Alhaji danladi Garba Pasali shi ne Shugaban kungiyar Yakin Neman Zaben Shugaban kasa Muhammad Buhari ta (BCO), a tattaunawar da ya yi wakilinmu, kan cece-kucen da ake yi kan maganar da Shugaba Buhari ya yi a kan wadansu matasan Najeriya, ya ce wadansu ’ya’yan Jam’iyyar PDP ne suka murguda abin da Shugaban kasar ya fada […]

’Yan PDP ne suka murguda maganar Buhari kan matasan Najeriya – danladi Pasali

Alhaji danladi Garba Pasali shi ne Shugaban kungiyar Yakin Neman Zaben Shugaban kasa Muhammad Buhari ta (BCO), a tattaunawar da ya yi wakilinmu, kan cece-kucen da ake yi kan maganar da Shugaba Buhari ya yi a kan wadansu matasan Najeriya, ya ce wadansu ’ya’yan Jam’iyyar PDP ne suka murguda abin da Shugaban kasar ya fada don bata shi. Kuma ya yi tsokaci a kan amincewar da Shugaba Buhari ya yi na sake tsayawa takara a zaben badi da yadda wadansu manya a Najeriya suka fito suna cewa ba za su goyi bayansa a zaben mai zuwa ba.

Aminiya: A ’yan kwanakin nan mutane suna ta cece-ku-ce kan bayanin da ake cewa Shugaba Buhari ya yi cewa matasan Najeriya cima-zaune ne, me za ka ce?

danladi Pasali: Wato duk wanda ya saurari abin da Shugaba Buhari ya ce kan wannan al’amari zai fahimci cewa ’yan adawa ne suka muguda bayanin da ya yi. Bayanin da suke cewa ya yi ba haka ya fada ba cewa ya yi akwai matasa da dama da sun ki karatu ko sana’a amma suna son su mallaki dukiya su yi gida da sauransu, Shugaba Buhari yana bayani ne kan irin wadannan matasa kuma abin da ya fada gaskiya ne ba karya ba. 

Irin wadannan matasa da yake nufi ne aka yi amfani da su a Boko Haram. Irinsu ne suke garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyuka na samun kudi cikin dare daya.

Babbar matsalar da ta sanya suka shiga cikin irin wadannan abubuwa akwai wadansu miyagu da suka sace kudin Najeriya suka kai kasashen waje suka boye, maimakon su bude manyan kamfanoni a Najeriya ko su karfafa wa matasa gwiwa su koma gona.

Wannan shi ne abin da Shugaba Buhari ya fito da shi ya sanya matasa suka koma gona. Don haka wannan magana, magana ce ta PDP domin idan ka dubi wannan magana, wani jigo a Jam’iyyar PDP ya fito ya ce wannan magana ta matasa da Buhari ya yi da PDP ta fito tana ta maganganu a kai, ba haka ya fada ba, babu inda Buhari ya yi amfani da kalmar malalata ko cima-zaune. 

Kuma masu cewa hankalin matasan kasar nan ya tashi kan wannan magana ta Shugaba Buhari ’yan adawa ne, kuma ba gaskiya suke fada ba, domin matasan kasar nan suna nan tare da Buhari. Ko a makon nan a Jigawa matasa sama da dubu 700 sun fito sun ce suna murna da amincewar da Shugaba Buhari ya yi cewa zai sake tsayawa takarar Shugaba kasa a badi.  Sai dai a ce wadansu kalilan mutane ’yan barandar barayin kasar nan ne suke adawa da shi, wato wadanda idan barayin suka sato kudin kasar nan suke ba su wani abu, su ne suka ta yada karairayi kan wannan magana.

 

Aminiya: A matsayinka na Shugaban kungiyar BCO ta yakin neman zaben Shugaba Buhari me za ka game da bayanin da ya yi cewa zai sake tsayawa takara a zaben badi?

danladi Pasali: Wato na farko za mu ce mun gode Allah, dama fafutikar da muke ta yi ke nan. Muna ta kira ga Shugaba Buhari ya amince ya sake tsayawa zaben badi, domin ba zai yiwu irin dimbin ayyukan da ya faro na raya kasa, a ce ba zai sake tsayawa takara a zaben badi ba. Don haka a wannan  kungiya a muka rika yawo a duk fadin kasar nan, muna shirya tarurruka da jerin gwano a wurare daban-daban, tare da yin kira a gidajen rediyo da jaridu kan Shugaba Buhari ya amince ya sake tsayawa takara a zaben badi.

Don haka mu muna ganin wannan amincewa da Shugaba Buhari ya yi, don sake tsayawa takara a zaben badi kamar addu’armu ce Allah Ya amsa.

 

Aminiya: A kwanakin baya wadansu tsofaffin Janar-Janar din soja a Najeriya, sun fito sun nuna cewa ba za su goyi bayan Shugaba Buhari ya sake tsayawa takara a zaben badi ba. Me za ka ce kan wannan mataki da tsofaffin Janar-Janar din suka dauka?

danladi Pasali: Abin da nake son ka gane shi ne dukan wadannan tsofaffin Janar-Janar da wadansu tsofaffin shugabanni da wadansu marasa kishin kasa, da ma ai ba su ne suka bai wa Shugaba Buhari zabe ba, talakawan Najeriya ne suka fito suka zabe shi Shugaban kasar nan, domin su ne suke son sa. Kuma dukan wadannan tsofaffin shugabanni da suke adawa da Shugaba Buhari kashi 80 bisa 100 ’yan Jam’iyyar PDP ne. Don haka ba wani abin mamaki ba ne, don sun fito sun ce ba za su amince Shugaba Buhari ya sake tsayawa takarar Shugaban kasar nan ba. 

Kuma ina son ka gane cewa binciken da wannan gwamnati take yi, kan cin hanci da rashawa da yadda wadansunsu ba sa biyan harajin kamfanoninsu wadannan abubuwa suna damunsu Bayan haka kuma a saninmu ne cewa rijiyoyin man wadansu daga cikinsu lokacinsu ya riga ya kare. Maganar sabunta wadannan rijiyoyin mai wani aiki ne mai wahalar gaske a wajensu a zamanin wannan gwamnati ta Shugaba Buhari.  Kuma idan ka dubi wadannan tsofaffin Janar -Janar rikice rikicen kabilanci da addini da ake fama da su a garuruwansu ana zargin suna da hannu a ciki. Don haka ba abin mamaki ba ne don sun fito sun ce ba za su amince Shugaba Buhari ya sake tsayawa takarar Shugaba kasar nan a zaben badi ba.

Idan ka lura duk mutumin da ya ce ba ya kaunar Shugaba Buhari, idan ka dube shi za ka ga ko tsohon barawo ne ko tsohon macuci ne, irin wadannan mutane ne ba sa son Buhari.

Don haka mu talakawan Najeriya da muke neman Shugaba Buhari ya kafa mana ginshiki a Najeriya, muke kaunarsa kuma za mu ci gaba da kaunarsa. Don haka a zaben badi  ina tabbatar maka cewa babu wani kokwanto cewa Shugaban kasa Buhari, zai sake lashe zaben kujerar shugabancin kasar nan. 

 

Aminiya: Idan muka dawo nan Jihar Filato me za ka ce kan sake fitowa takara da Gwamna Simon Bako Lalong ya yi a badi?

danladi Pasali: Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ina tabbatar maka cewa a tarihin jihar, bayan tsohon Gwamnan Jihar Solomon Lar ba a taba samun Gwamnan da hada kan jama’ar jihar kamar Gwamna Simon Lalong ba. Sakamakon kokarin da Gwamna Lalong ya yi yau jama’a ko’ina a Najeriya da kasashen waje suna son su zo Jihar Filato, domin gudanar da harkokinsu. Don haka idan Gwamna Lalong ya ce bai tsaya takarar Gwamnan Jihar Filato a zaben badi ba, kamar ya ci amanar al’ummar Jihar Filato ne. Don haka muna tare da shi kuma ina tabbatar maka a zaben Gwamna na badi babu gurbi a kujerar Gwamnan Jihar Filato, domin mu ba mu san kowa ba, sai Gwamna Lalong, domin yau a Jihar Filato kowa yana shiga duk inda ya ga dama. 

A zamanin gwamnati PDP da ta gabata a Jihar Filato, abin ba haka yake ba, a lokacin  a Bahaushe Musulmi yana tsoron ya shiga unguwannin Kiristoci. Kiristoci suna tsoron su shiga unguwannin Musulmi, amma yanzu duk wannan tsoro ya kau. Don haka ko’ina a Jihar Filato, Musulmi da Kirista suna zaune lafiya sun zama ’yan uwa kamar yadda ake a da. Don haka wannan abu na kawo zaman lafiya da Gwamna Lalong ya yi a Jihar Filato, ya nuna shi ne shugaba na kwarai. 

 

Aminiya: A karshe wane sako kake da shi zuwa ga al’ummar Najeriya?

danladi Pasali: Sakona ga jama’ar Najeriya shi ne Shugaban kasa Buhari ya bude mana hanyoyi na ci gaba da dama, musamman shirin bayar da rancen noma na Babban Bankin Najeriya. A yanzu maganar da nake gaya maka a karkashin wannan kungiya kadai a shirin harkokin noma da muke yi, mun dauki matasa miliyan daya da muka hada hannu da Ma’aikatar Gona ta Tarayya da Babban Bankin Najeriya don bai wa matasan rancen noma a daminar bana. Wani babban abin alheri da wannan gwamnati ta yi, yanzu idan ka tafi kasashen waje har Afirka ta Kudu za ka ga shinkafar da aka noma a Najeriya ana sayarwa, ka ga wannan babban abin alfahari ne ga Najeriya. 

Bayan haka a tafiyar da Shugaba Buhari ya yi zuwa kasashen waje a ’yan kwanakin nan, ya je ya kulla wata yarjejeniya da kamfanin mai na Shell, inda za su zo Najeriya su sanya hannun jari na Dala biliyan 15 don kafa matatar mai a Najeriya. Wannan ya nuna cewa har yanzu kasashen duniya suna girmama Shugaba Buhari suna ganin darajarsa. 

Kuma yanzu kudaden ajiyarmu na asusun waje sun kai sama da Dala biliyan 48, wannan ne ya jawo kasashen duniya suke rige-rigen zuwa don zuba jarinsu a kasar nan.