’Yan PDP ne yawanci suka ci zabe a APC – Farfesa Alkali

Farfesa Rufa’i Ahmad Alkali shi ne mai bai wa shugaban kasa Jonathan shawara a kan al’amuran siyasa, Aminiya ta zanta da shi a kan yadda jam’iyyar PDP ta ji game da sakamakon zabe da kuma canja matsayinta zuwa ta ’yar adawa. Aminiya: Yaya jam’iyyarku ta PDP ta ji game da sakamakon zabubbukan da aka yi?Farfesa […]

’Yan PDP ne yawanci suka ci zabe a APC – Farfesa Alkali

Farfesa Rufa’i Ahmad Alkali shi ne mai bai wa shugaban kasa Jonathan shawara a kan al’amuran siyasa, Aminiya ta zanta da shi a kan yadda jam’iyyar PDP ta ji game da sakamakon zabe da kuma canja matsayinta zuwa ta ’yar adawa.

Aminiya: Yaya jam’iyyarku ta PDP ta ji game da sakamakon zabubbukan da aka yi?
Farfesa Rufa’i Alkali: To mun gode wa Allah mai kowa mai komi, ana cewa za a yi zabe,za a yi zabe, ga shi Allah Ya nuna mana an yi zaben 2015 an gama lafiya, sai mu kara gode wa Allah da Ya nuna mana wannan lokaci, mu kuma gode masa da ya takaita mana matsaloli da kan biyo bayan dukkan zabubbuka.
Aminiya: Jamiyyarku ta PDP ta yi ta kurarin za ta samu gagarumin nasara a zaben sai ga akasin hakan, me kake jin ya jawo mata faduwa?
Farfesa Rufa’i Alkali: Ka san dan Adam na nasa Allah na nashi, dama ko a lokacin da muke yakin neman zabe ai ba mu ce mu ne za mu bai wa kanmu nasara ba, mun dogara ga Allah ne, iyaka dama abin da demokoradiyya ta gada, ta koyar, ta kuma saba a kai shi ne ka nemi goyon bayan jama’a, hakan ne kuma muka yi, an yi kamfen daidai gwargwado, to tunda Allah Ya yi nasa hukuncin ai zai yi wuya kuma mutum ya ce zai yi fushi da hukuncinSa.
Aminiya: A baya jam’iyyar PDP ta yi hasashen za ta shekara hamsin a kan mulkin kasar nan, to ga shi yanzu wannan abu ya fita a hannunta, ya zama a karkashin adawa zai kasance muku, za ku iya jurewa kuwa?
Farfesa Alkali: To kamar yadda ka sani bayanin cewa jam’iyya za ta yi shekara da shekaru tana mulki, fata ne! kuma fata ba laifi ba ne, babu wanda zai so ya yi wa mahaifiyarsa ko mahaifinsa fatan mutuwa, haka nan ba dan siyasan da zai yi wa jam’iyyarsa fatan gazawa ko lalacewa, saboda haka dole ne a bai wa jama’a azama, a nuna masu hanya su bi, saboda idan ka nuna musu cewa za ta rushe nan da shekara biyu to wane ne zai bi, wannan dai fata ne. Sai dai fa kar ka manta, su wadanda suka ci nasarar a cikin wata jam’iyyar ai yawancinsu ’ya’yan PDP ne, sauya sheka kawai suka yi. Ba sai an kai ka da nisa ba, idan ka dubi Sakkwato wanda ya ci zaben gwamna a wajen Honorabul Aminu Tambuwal ai dan PDP ne, a jihar Kebbi Sanata Bagudu shi ma dan PDP ne, idan ka dubi na Katsina Masari dan PDP ne, ya yi shugaban Majalisar wakilai a jam’iyyar, a Kaduna Nasiru Elrufa’i shi ma dan PDP ne, ya yi minista a karkashinta. A Adamawa Bindow dan PDP ne, yanzu haka ma kan kujerarta ya ke a sanata, na Binuwai Samuel Otu shi ma dan PDP ne, ya yi sakataren jiha na jam’iyyar, ya kuma yi National Auditor na PDP, a Jihar Taraba A’isha ita ma ’yar PDP ce, a kai ta zama Sanata, wannan dai na takaita maka ne kawai.
Aminiya: To bayan wadanda ka lisafto sun samu nasara a kan sun sauya sheka, sai ga shi har yanzu wadansu na ci gaba da ficewa daga cikin jam’iyyar, hakan ba zai shafe PDP daga doron kasa ba kuwa, musamman a nan Arewa?
Farfesa Rufa’i Alkali: Ka san kowa yana da dalili ko manufa na shiga jam’iyya ko ficewa daga cikinta, to ni ba zan yi magana a madadin wadansu ba, illa iyaka kowa yana da buri ko manufa na kasancewarsa a jam’iyya, sai dai ka sani, abin da ya ba ka mamaki an ce wata rana shi zai ba ka tsoro
Aminiya: Kusan daukacin gwamnonin PDP, koma a ce wadanda suka tsayar takara a nan Arewa sun sha kasa in banda na jiharka ta Gombe, me kake jin ya kawo masa nasarara?
Farfesa Alkali: To na hakikance shi ya tashi tsaye kuma tsayuwar daka, sannan ya dauki karin darasi daga yadda sakamakon zaben shugaban kasa ya kasance, ya kuma samu goyon bayan ’yan jam’iyya ta kowane bangare, na tabbata hakan ya kawo masa sassauci, kuma mu kanmu hakan zai kara mana darasi da za mu dauka, musamman a zabubbuka na jihohi da ke tafe, saboda akwai jihohi kamar bakwai da ba a yi zaben gwamna ba, akwai Osun da Ekiti da Ondo da Edo da Anambra da Kogi, na tabbata dole a samu karin darasi a game da su.
Aminiya: A karshe wani labari da ke yawo a wannan makon shi ne wanda ake cewa Shugaban kasa ya bayyana rashin gamsuwarsa a kan yadda aka tafiyar da kudin kamfen kuma zai yi bincike a kai, ya kuka ji waannan labara?
Farfesa Alkali: Mutane dama sun saba kitsa labari daga cikin dakunansu, sannan kuma kasancewar Allah Ya ba su damar samun kafofi da suke ya da labaran. Ribar dimokoradiyyar ke nan, kowa na da hurumin fadin albarkacin bakinsa. Sai dai fa kar ka manta, ya kamata kafin a yada labari a binciki sahihancinsa tukuna, musamman ma idan zai shafi cin mutuncin wani ko wadansu. Duk wanda zai ce maka za a kashe kudi kamar tiriliyan biyu a kamfen wanda ya kai matsayin daya bisa biyu na kasafin kudin Najeriya gaba daya, ai ya kamata idan mai fada ya zama mahaukaci bai kamata mai sauraro kuma ya kasance shi ma mahaukaci ba. Abu na biyu kuma ai kowa ya san cewa shi siyasa idan za ka yi shi al’amari ne na kasada wanda dole sai an yi asara a ciki, ashe zai yi wuya idan ba ka samu nasara a cikinta ba, ka ce za ka bukaci a mayar maka da abin da ka kashe.