‘Yan PDP sun yi zanga-zanga a ofishin Amurka da Birtaniya a Abuja
Shugabannin jam’iyyar adawa ta PDP tare da mambobin jam’iyyar sun gudanar zanga-zangar lumana saboda zargin jam’iyyar APC da rashin tabuka komai a kan matsalolin da kasar ke fuskanta. Shugaban PDP na kasa Uche Secondus, da dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar Peter Obi a zaben 2019, ne suka jagorancin zanga-zangar lumana, zuwa ofishin jakadancin […]
Zanga-zangar PDP
Shugabannin jam’iyyar adawa ta PDP tare da mambobin jam’iyyar sun gudanar zanga-zangar lumana saboda zargin jam’iyyar APC da rashin tabuka komai a kan matsalolin da kasar ke fuskanta.
Shugaban PDP na kasa Uche Secondus, da dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar Peter Obi a zaben 2019, ne suka jagorancin zanga-zangar lumana, zuwa ofishin jakadancin Birtaniya da na Amurka da ke Abuja inda suka mika takardar kokensu.
Shugabannin PDP sun bukaci a yi adalci a hukuncin kotun koli wajen karbe kujerar Gwamnan Imo na PDP Emeka Ihedioha, aka bai wa dan takarar Gwamnan APC.