’Yan PDP sun zame wa gwamnatin Buhari alakakai-Onochie
Mai Taimaka wa Shugaba Muhammadu Buhari Kan Kafofin Sa Da Zumunta, Misis Laurette Onochie ta ce ’yan jam’iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC sun zame wa gwamnatin Buhari karfen kafa. Onochie ta yi furucin ne a yau a Abuja yayin taron wata kungiyar hadin kai wacce atakaice ake kira PSF. Ta ce […]

Mai Taimaka wa Shugaba Muhammadu Buhari Kan Kafofin Sa Da Zumunta, Misis Laurette Onochie ta ce ’yan jam’iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC sun zame wa gwamnatin Buhari karfen kafa.
Onochie ta yi furucin ne a yau a Abuja yayin taron wata kungiyar hadin kai wacce atakaice ake kira PSF.
Ta ce wadanda suka sauya shekar sun kai kashi 50 cikin dari a cikin gwamnatin kuma sun mamaye kowane bangare.