’Yan PDP za su rasa madogara in ta fadi a zabe – Sanata Zabgayi

Sabon dan Majsalisar Dattawa mai wakiltar Neja ta Gabas, kuma tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Dokta Shem Zabgayi Nuhu ya bayyana fatar Jam’iyyar PDP ta ci gaba da lashe zabubbukan da za a gudanar a badi.Dokta Zabgayi ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a gidan gwamnati yayin da tawagar Jam’iyyar PDP a karkashin jagorancin […]

’Yan PDP za su rasa madogara in ta fadi a zabe – Sanata Zabgayi
’Yan PDP za su rasa madogara in ta fadi a zabe – Sanata Zabgayi

Sabon dan Majsalisar Dattawa mai wakiltar Neja ta Gabas, kuma tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Dokta Shem Zabgayi Nuhu ya bayyana fatar Jam’iyyar PDP ta ci gaba da lashe zabubbukan da za a gudanar a badi.
Dokta Zabgayi ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a gidan gwamnati yayin da tawagar Jam’iyyar PDP a karkashin jagorancin shugabanta na jihar Alhaji Mahmud Abdul-Rahman Enagi ta raka shi domin gabatar da takardar shaidar lashe zaben da domin sa albarka.
Ya ce idan har aka rasa hakan ba ’ya’yan jam’iyyar za su rasa madogara a rayuwa ganin cewa da dama daga cikinsu sun dogara ga gwamnati mai ci ko wasu kusoshinta domin rufa wa kawunansu asiri.
Sanata Shem Zabgayi ya ce turjewar da Jam’iyyar PDP ta samu a zaben cike gurbin da aka yi a shiyyar ba ta rasa nasaba da dangantaka mara inganci tsakanin zababbun jami’ai da jama’ar da suka zabe su, inda jami’an ba su sake waiwayar masu zabe sai bukatar zabubbuka sun taso sannan ake ziyartar su babu dare babu rana.
Ya shaida wa Gwamnan Jihar Neja Alhaji Mu’azu Babangida Aliyu cewa, “Sai da na shiga tsakanin wani kansila da jama’arsa a karamar Hukumar Shiroro inda suka shaida min cewa rabonsu da ganinsa tunda ya ci zabe, sai da muka je neman kuri’unsu a zaben cike-gurbin da ya gabata wanda ya yi zafi, kuma duk da mun samu nasara da sauran rina a kaba. Haka lamarin yake a tsakanin shugaban jam’iyya na mazabar da jama’arsa.”