’Yan rakiyar amarya 19 sun mutu a hatsarin mota a Zamfara

“Motar ta faɗo ne daga saman gada ta nutse a ruwa. Da aka ciro su, mutum 19 daga cikinsu sun mutu, maza, mata da yara,” a cewar ɗan uwan amaryar.

’Yan rakiyar amarya 19 sun mutu a hatsarin mota a Zamfara

Aƙalla mutane 19 ne suka mutu a yayin da suka ɗauko wata amarya zuwa ɗakin mijinta bayan motarsu ta faɗa a ƙarƙashin gadar Gwalli da ke yankin Fass a Ƙaramar Hukumar Gummi a Jihar Zamfara.

Lamarin ya faru ne da yammacin Asabar da misalin ƙarfe 4:45 na yamma, lokacin da motar, da ke ɗauke da maza da mata da yara ta faɗo daga saman karyayyiyar gadar, ta nutse a cikin ruwa, kamar yadda kafar SoalceBase ta ruwaito.

Wani ɗan uwan amaryar, Babangida Halifa Ibrahim Fass, wanda ya rasa ’yan uwa a cikin hatsarin, ya ce hatsarin ya faru ne a lokacin da ake kai ’yar uwarsa amarya gidan mijinta  da ke Jega a Jihar Kebbi.

Ya ce, “Motar ta faɗo ne daga kan gada ta nutse a ruwa. Da aka ciro su, mutum 19 daga cikinsu sun mutu, maza, mata da yara.”

A ranar Lahadin nan ake sa ran yin jana’izar su, kuma an bayyana cewa mahaifin amaryar shi ne tsohon ɗan majalisar jihar, Marigayi Sheikh Dauda Fass.

Gadar Gwalli, wadda ke haɗa ƙauyukan Gwalli, Yar Gusau da Fass, ta daɗe a lalace ba tare da an gyara ta ba.

An fara gyara ta a lokacin mulkin tsohon gwamna Abdulaziz Yari, amma ruwan sama ya sake lalata ta tun kusan shekaru bakwai da suka gabata.

A bana ma, al’ummar yankin sun yi ƙoƙarin cike sasanta da suka zaizaye da yashi domin rage haɗarin, amma duk da haka gadar ta sake karyewa.

Wasu mazauna ƙauyen sun ce lalacewar gadar ta jawo musu wahala musamman a lokacin damina, inda ake tsoron ambaliyar ruwa ta tafi da mutane.

Babangida ya ɗora alhakin matsalar a kan sakacin gwamnati, yana cewa: “Tun lokacin muna cikin wahala. Wasu lokuta har ta cikin rafi muke ƙetarawa domin kai gawa maƙabartar. Mun taɓa cike buhunan shinkafa da na siminti da yashi don gina gadarmu.”

Mutanen yankin sun roƙi gwamnatin jihar da ta tarayya da su gaggauta gina sabuwar gada kafin irin haka ya sake faruwa.

Sun ce wannan lamari ya sake nuna yadda jama’ar Zamfara ke rayuwa cikin tsoro da wahala duk da iƙirarin gwamnati na gyara muhimman hanyoyi a ƙauyuka.

Da aka tuntubi mai magana da yawun gwamna, Mustapha Jafaru Ƙaura, ya fara cewa bai san da kauyen ko kuma wannan lamarin ba, amma daga bisani ya yi alƙawarin yin bincike.