An cafke dan shekara 80 cikin ’yan fashin da suka kashe dan sanda a Ibadan
Sun bayyada suka bindige ASP Ogunleye Olufemi Daniel a lokacin harin
Wasu mutum uku da suka furta cewa su ne suka bindige wani Mataimakin Sufeton ’Yan Sanda (ASP) Ogunleye Olufemi Daniel a Unguwar Ori-Agogo a yankin Odo-Ona Kekere cikin birnin Ibadan na Jihar Oyo sun shiga hannu.
Mutanen da suka hada da wani mai shekara 80 da masu shekaru 25 da 26, sun shaida wa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo cewa sun hallaka dan sandan ne a wani harin fashi da suka kai unguwar a karshen watan Afrilu.
- Hijirar ’yan bindiga daga Zamfara zuwa Katsina ta tayar da kura
- Bankin Musulunci zai ba wa Afirka $8bn domin noma da raya karkara
Kakakin rundunar, SP Adewale Osifeso, wanda ya gabatar da su a madadin kwamishinan ’yan sandan jihar Adebowale Williams ga ’yan jarida a ranar Juma’a a Ibadan, ya ce barayin sun yi ikirarin ne bayan da rundunar ta kama su..
A cewarsa, wadanda ake zargin sun bindige ASP Ogunleye Olufemi Daniel da ke aiki a sashen binciken manyan laifuka na (CID) ne a lokacin da suka kai harin a unguwar ta Ori-Agogo inda yake zaune tare da iyalinsa.
Ya ce jim kadan bayan samun labarain harin ne sashen binciken manyan laifuka na rundunar ya kama aikin bin diddigi da ya kai ga kama wadannan mutane uku da kowannensu ya bayyana irin rawar da ya taka wajen kisan da suka yi wa dan sandan.
’Yan sandan sun nuna wasu wayoyin hannu mallakar marigayin da wata karamar bindiga da mota da aka samu a tare da barayin.
Akwai kuma wata mata da ake yi wa lakani da ‘Iya-Alaye’ da aka nuna su tare da ’yan fashi, wadda kakakin ’yan sandan ya ce an kama ta ne bayan ’yan fashin sun ambaci sunanta a matsayin wacce take sayan gwalagwalan sarkokin wuya da suke kai mata idan sun sato.