’Yan sanda 1,000 aka girke a bikin binne Uwargidan Awolowo
A ranar Larabar da ta gabata ce aka yi bikin binne uwargidan Firimiyan Kudu maso yamma, Mama Hannah Awolowo, wacce ta mutu a watan Satumba da ya gabata, inda taron ya gudana cikin cikakken tsaro domin jami’an ’yan sanda 1,000 aka girke a garin na Ikenne, baya ga sajoji da sauran jami’an tsaro daban-daban.Kwamishinan ’yan […]
A ranar Larabar da ta gabata ce aka yi bikin binne uwargidan Firimiyan Kudu maso yamma, Mama Hannah Awolowo, wacce ta mutu a watan Satumba da ya gabata, inda taron ya gudana cikin cikakken tsaro domin jami’an ’yan sanda 1,000 aka girke a garin na Ikenne, baya ga sajoji da sauran jami’an tsaro daban-daban.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Ogun, Abdulmajeed Ali ya shaida wa Aminiya cewa sun girke ‘yan sanda har guda 1000 ne domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a masu halartar bikin, kana yana daga cikin abin da suka tattauna da Sufeto-Janar, Solomon Arase a ziyarar da ya kai jihar a makon jiya.
Marigayiyar wadda ta mutu tana da shekaru 99 a duniya, an binne ta ne a daidai ranar da take cika shekara 100 a duniya.
A jawabinsa a madadin Shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin zuwansa da kansa, Shugaban Majalisar Dattawa, Abubakar Bukola Saraki, ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa wadda ta ba da gudunmuwa wajen gina kasar nan wajen kasancewarta a matsayin kasa-daya-al’umma daya. Ya kuma yi kira ga iyalan gidan na Awolowo da su rike kambin gidan kamar yadda shi maigidan da uwargidansa suka yi.
Kafin mutuwarta, Hannah Awolowo ’yar siyasa ce kuma shahararriyar ’yar kasuwa domin ita ce farkon dillaliya mai rarraba tabar sigari a Kamfanin Tobaco, kana ita ce ta fara shigowa da leshi a kasar nan. Kana marubuciya ce a jaridar Nigerian Tribune, wadda maigidanta ya kafa a 1949.
Manyan kaki da suka ziyarci garin na Ikenne sun hada da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, wanda suriki ne a gidan na Awolowo. Sauran sun hada da Shugaban Majalisar Dattawa, Abubakar Bukola Saraki da uban jam’iyyar APC, Alhaji Ahmad Bola Tinunbu da Gwamnoni 16 wadanda suka hada da na Zamfara, Kaduna, Imo, Sakkwato, Ondo da ministoci da dai sauransu.