’Yan sanda 2 sun gamu da ajalinsu a Abiya
Wasu jami’an ’yan sanda biyu da ke aiki da caji ofis na Ogbor Hill da ke garin Aba, Jihar Abiya sun gamu da ajalinsu a makon nan; a yayin da suke kan hanyarsu ta amsa kiran kawo daukin agajin gaugawa da aka kirawo ofishin su.Jami’an suna kan hanyarsu, kafin su isa wurin ake kyautata zaton […]
Wasu jami’an ’yan sanda biyu da ke aiki da caji ofis na Ogbor Hill da ke garin Aba, Jihar Abiya sun gamu da ajalinsu a makon nan; a yayin da suke kan hanyarsu ta amsa kiran kawo daukin agajin gaugawa da aka kirawo ofishin su.
Jami’an suna kan hanyarsu, kafin su isa wurin ake kyautata zaton ’yan fashi da makami ne, da ke tafka halin nasu a layin Ukaegbu, kan hanyar Ikot-Ekpene suka kashe su. An yi zargin ’yan fashin ne suka yi wa jami’an tsaron da suka kawo daukin kwanton bauna suka aika su lahira.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Abiya, DSP Ezekiel Onyeka, ya tabbatar wa Aminiya afkuwar lamarin, sai dai ya sakaya sunayen wadanda suka rasa rayukan nasu, inda ya ce: “Tabbas ’yan fashi da makamin da suka yi fashi a layin Ukaegbu ne suka kashe su, domin lokacin da suka ji motsin zuwan ’yan sandan; wasu daga cikin barayin suka yi wa jami’anmu kwanton bauna, suka harbe su.”
Ya ci gaba da cewa: “Yadda abin ya faru shi ne, kirawo caji ofis na Ogbor hill aka yi, aka shaida masu cewa ga abind a ke faruwa. A kokarin kai dauki ne da ’yan sandan suka yi, kaddara ta riga fata, ta fada masu; suka gamu da ajalinsu. Sai dai ’yan fashin sun arce, ba a yi katarin kama ko daya daga cikinsu ba.”