‘’Yan Sanda 20 Aka Ji Wa Rauni A Zanga-zangar Gombe’
An kwantar da ’yan sandan da aka jikkata a zanga-zangar a asibitin gidan gwamnati
Kwamishinan ’Yan Sandan Gombe, Hayatu Usman, ya bayyana cewa an jikkata jami’ansa 20 a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a jihar.
Ya ce an yi arangama sosai inda aka samu asarar dukiyoyin gwamnati da na al’umma, amma da taimakon sauran hukumomin jami’an tsaro an shawo kan lamarin tare da dawo da zaman lafiya a jihar.
Kwamishinan ya bayyana cewa duk da haka bai samu rahoton rasa rai ko daya ba sakamakon zanga-zangar.
Amma ya ce zaman lafiya ya dawo a jihar, al’umma sun ci gaba da hada-hadarsu, ’yan kasuwa sun bude shagunansu, sannan jami’an tsaro suna ci gaba da sintiri da kula da abin da ka iya je ya dawo.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Zanga-Zanga Ke Durkusar Da Sana’o’i Da Tattalin Arziki
- Rasha ta nesanta kanta da zanga-zangar Najeriya
Da yake jawabi bayan kammala zaman majalisar tsaron jihar a ranar Litinin, Hayatu Usman ya bayyana cewa an kwantar da jami’an ne a asibitin gidan gwamnatin jihar.
Ya kuma yaba wa al’ummar gari musamman wasu iyayen kirki da suka taimaka musu wajen dawo da kayayyakin da wasu daga cikin ’ya’yansu suka sace a lokacin zanga-zangar.