’Yan sanda 3 da dan fashi daya sun mutu a musayar-wuta a Legas

Wani gungun da ake zargin ’yan fashi da makami ne sun bude wa ’yan sandan sintiri wuta a yankin Ijora Olopa da ke Legas, inda suka kashe uku daga cikin ’yan sandan nan take. ’Yan fashin, wadanda suke gudanar da harkarsu a kan babura, sun bude wa’yan sandan wuta ne a yayin da suka yi […]

’Yan sanda 3 da dan fashi daya sun mutu a musayar-wuta a Legas
’Yan sanda 3 da dan fashi daya sun mutu a musayar-wuta a Legas

Wani gungun da ake zargin ’yan fashi da makami ne sun bude wa ’yan sandan sintiri wuta a yankin Ijora Olopa da ke Legas, inda suka kashe uku daga cikin ’yan sandan nan take.
’Yan fashin, wadanda suke gudanar da harkarsu a kan babura, sun bude wa’yan sandan wuta ne a yayin da suka yi arba da su.  Aminiya ta kalato cewa daya daga cikin ’yan sandan da suka rage ya kashe daya daga cikin ’yan fashin a yayin da ya mayar da wuta a kansu a lokacin da suke tserewa.
An fahimci cewa ’yan fashin sun yaudari ’yan sandan, wadanda suke daga ofishin sashen C da ke Surulere ne, dangane da irin suturar da suke sanye da ita ta kaftani da wando.  
Wata majiya daga ’yan sandan a Ijora Olopa ta bayyana cewa an sami wata bindiga mai barin wuta a wurin da aka yi artabun, kuma an kwashen gawawwakin ’yan sandan da ta dan fashin an kai dakin ajiye gawarwaki.
Kwamishinan’yan sanda na jiha Umar Manko ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce ’yan fashin sun yi amfani da lokacin ruwan sama ne suka farmaki ’yan sandan, suka kashe uku daga cikinsu, suka ji wa daya rauni, amma direbansu bai sami ko kwarzane ba.