’Yan sanda 5 sun rasu a hatsarin mota a Kano

Jami’an na kan hanyarsu ta dawowa daga aikin zaɓen Jihar Edo da aka kammala.

’Yan sanda 5 sun rasu a hatsarin mota a Kano

Hukumar Kiyaye Hadura ta Ƙasa (FRSC) a Jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar wasu’yan sanda guda biyar a wani hatsari da ya rutsa da su.

Hatsarin ya faru ne a kan hanyar Zariya zuwa Kano a ƙauyen Karfi.

Kakakin hukumar a Kano, ya ce, rundunar ‘yan sandan ƙaramar hukumar Kura ne, suka bayar da rahoton hatsarin.

Ya ce ya rutsa da motoci guda biyu: tirela da kuma wata mota ƙirar Toyota Hummer mai lamba 14B101KN, mallakin Kano Line.

Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:15 na safe kuma ya rutsa da mutum 15.

Sai dai ya ce mutum biyar sun mutu, yayin da wasu 10 suka samu raunuka.

Waɗanda hatsarin ya rutsa da su ‘yan sandan ne da ke kan hanyarsu ta dawowa daga aikin zaɓen da aka kammala a Jihar Edo.

Binciken farko na FRSC ya nuna cewa hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce ƙima.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7