’Yan sanda a Amurka sun yi murabus don nain bakar fata magajiyar gari
A ranar Litinin da ta gabata ne aka samu ’yan sanda kashi huu cikin biyar da ke aiki a wani karamin gari mai suna, Parma, a Jihar Missouri ta kasar Amurka suka ajiye aikinsu gabanin fara aikin wata magajiyar gari bakar fata mai suna, Mayor Tyrus Byrd. Hazalika, lauyan gwamnatin birnin da akawu da kuma […]
A ranar Litinin da ta gabata ne aka samu ’yan sanda kashi huu cikin biyar da ke aiki a wani karamin gari mai suna, Parma, a Jihar Missouri ta kasar Amurka suka ajiye aikinsu gabanin fara aikin wata magajiyar gari bakar fata mai suna, Mayor Tyrus Byrd.
Hazalika, lauyan gwamnatin birnin da akawu da kuma mai kula da hukumar ruwan shan birnin su ma sun yi murabus, kamar yadda kafar yaa labarai ta The Independent ta bayyana.
Magajin gari mai barin gado Randall Ramsey wanda ya shugabancin birnin na tsawon shekara 37, kuma ya ce ma’aikatan da suka yi murabus in ba su bayyana dalilinsu na yin hakan ba.
Ba a dai fahimci dalilin da ya sa hakan ba, amma wasu ma’aikata sun hakan bai rasa nasaba da “kiyaye lafiyarsu.”
Kodayake, mazauna birnin Parma sun bayyana wa manema labarai cewa ba su da wata damuwa saboda hakan. Kuma a cewarsu da ma can ’yan sanda da ke aiki a birnin sun yi yawa. “Ba na ganin matakin da suka auka ya dace musamman ma idan aka yi lakari da cewa ba su bayar da dalilin da suka sanya su uin hakan ba,” inji wani mazaunin birnin Parman.
Masana dai na danganta matakin da wariyar launin fata, musamman ma ganin hakan ya faru ne a jihar da ta yi kaurin suna wajen samun tashin hankula masu nasaba da wariyar launin fata a baya. Inda ko a farkon watan jiya, sai da wani bincike da ake gudanarwa a kan kisan wani saurayi bakar fata da wani an sanda farar fata ya yi bara a garin Ferguson, na Jihar Missourin ya bankao hujjoji masu imbin yawa cewa ‘yan sanda da jami’an kotu a garin na nuna wariyar launin fata.