’Yan sanda a Brazil sun gudanar da yajin aikin kwana daya
Dubban ’yan sanda ne suka shiga wani yajin aiki shekaranjiya Laraba a jihoji 14 na kasar Brazil a dalilin rashin karin albashi. Yajin aikin na zuwa ne kasa da wata daya gabanin fara wasan cin kofin kwallon kafa na duniya, wanda ake ganin zai kawo cikas ga ci gaba da shirye-shiryen fara gasar.Yajin aikin ya […]
Dubban ’yan sanda ne suka shiga wani yajin aiki shekaranjiya Laraba a jihoji 14 na kasar Brazil a dalilin rashin karin albashi.
Yajin aikin na zuwa ne kasa da wata daya gabanin fara wasan cin kofin kwallon kafa na duniya, wanda ake ganin zai kawo cikas ga ci gaba da shirye-shiryen fara gasar.
Yajin aikin ya shafi da dama daga cikin garuruwan da ke karbar bakuncin gasar ciki har da garin Sao Paulo, inda a nan ne aka shirya fara gasar a ranar 12 ga watan gobe.’Yan sandan na neman karin albashi da kashi 80 cikin 100.
Kodayake, tun kafin wannan yajin aikin Hukumar da ke Kula da Harkokin Kwallon kafa ta Duniya (FIFA) ta bayyana rashin gamsuwarta ga yadda kasar take gudanar da shirye-shiryen karbar bakuncin gasar. Inda ta bukaci kasar da ta kammala dukkannin ayyukan filayen wasannin da za a gudanar da gasar a ciki, kafin karshen watan Disamban bara. Amma sai a farko-farkon watannan ne aka kammala ayyukan wasu daga cikinsu.