’Yan sanda a Katsina sun kama jabun sojan sama

Rundunar ’yan sanda a Jihar Katsina ta kama wani matashi mai suna Nasiru Abu dan kimanin shekara 34 mazaunin Ramin Kura da ke Unguwar Filin Polo a cikin garin Katsina, bisa zarginsa da take yi a kan amfani da kakin soja yana yi wa jama’a sojan-gona da sunan cewa shi sojan sama ne. Ta haka […]

’Yan sanda a Katsina sun kama jabun sojan sama

Rundunar ’yan sanda a Jihar Katsina ta kama wani matashi mai suna Nasiru Abu dan kimanin shekara 34 mazaunin Ramin Kura da ke Unguwar Filin Polo a cikin garin Katsina, bisa zarginsa da take yi a kan amfani da kakin soja yana yi wa jama’a sojan-gona da sunan cewa shi sojan sama ne. Ta haka yake amfani da wannan dama yana karbar wasu abubuwa daga hannun jama’a.

Kamar yadda binciken ’yan sanda ya nuna, shi dai wannan matashi, an kore shi daga aikin sojan sama saboda wasu laifuffuka da aka same shi da su, wanda hakan ne ya ba shi damar yin amfani da kakin domin ban tsoro tare da yaudarar jama’a.

An kama Nasiru ne ta sanadiyyar dukan wata mai suna Sa’adatu Muhammad Bugaje da ya yi, wadda ke zaune a Unguwar kofar kaura Katsina. Kazalika ya karbe mata wayar hannu kirar Tecno K7, wacce aka kiyasta kudinta Naira dubu 33 da zoben gwal na Naira dubu 39, tare da tsabar kudi Naira dubu biyu.

Sai dai kamar yadda Aminiya ta kalato daga wata majiya, dama tare suke da ita wannan mata, sabani ne ya shiga tsakani har suka kai ga wannan hali, inda ta kai kara ga jami’an tsaron. Haka kuma an zargi Nasiru cewa ya karbi buhunan shinkafa biyar, wadanda kudinsu suka haura Naira dubu sittin daga hannun wani dan kasuwa mai suna Jariri Dando da ke Unguwar kofar Guga Katsina.

Kamar yadda jami’an suka ce, a binciken da suka yi sun samo kakin soja 4, hula hana Sallah 2, maballai 49, baje 9 da kuma alamar mukamin Laftanar 3, dukkansu na sojan sama. Haka kuma an samu layukan waya 10 da mota kirar Golf mai lamba AWK811HM. Sun bayyana cewa da zarar sun gama bincike za su mika wanda ake zargin zuwa kotu.