’Yan sanda a Kenya sun kama mutane 627 bayan harin gurnet
’Yan sanda a kasar Kenya sun cafke mutane 627, bayan wani harin gurnet da aka kai a gundumar Eastleigh ranar Litinin da ta gabata wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane shida, wasu da dama kuma suka jikkata.Ministan Harkokin Cikin Gidan kasar Joseph Ole Lenku ya bayyana harin da “dabbamci wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen […]

’Yan sanda a kasar Kenya sun cafke mutane 627, bayan wani harin gurnet da aka kai a gundumar Eastleigh ranar Litinin da ta gabata wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane shida, wasu da dama kuma suka jikkata.
Ministan Harkokin Cikin Gidan kasar Joseph Ole Lenku ya bayyana harin da “dabbamci wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen da basu ji ba, ba su gani ba.” Ya kuma bayyana mutanen kasar Kenya da masu kaunar zaman lafiya.
Harin dai ya yi kama da aikin kungiyar Al-Shabab ko al-kaeda da suke da sansani a kasar Somalia, amma har zuwa lokacin hada wannan rawotan ba daya daga cikin kungiyoyin biyu da ta ce wani abu game da harin.
Maharan dai sun hari wani asibiti ne da wasu guraren cin abinci guda biyu da ke gundumar ta Eastleigh wacce wasu suke kira “karamin garin Mogadishu” saboda kasancewar dinbim ‘yan Somalia da ke zaune a gundumar.
Idan ba a manta ba dai, a watan Satumbar bara ne wasu maraha suka kai wani mummunan hari a cibiyar kasuwancin nan ta Westgate, inda mutane 67 suka rasa rayukansu.
Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya ce hare-haren ta’addancin sun fara barazana ga yadda baki ‘yan kasashen waje ke tururuwan ziyartar kasar Kenya don yawon bude ido wanda ke samar wa kasar kudaden shiga masu kauri.