’Yan sanda a Sakkwato sun raba wa iyalan mamatansu Naira Miliyan 25
Rundunar ’yan sanda a Jihar Sakkwato ta raba wa iyalan ’yan sadan da suka rasa rayukansu a lokacin aiki sama da Naira miliyan 25, domin kawo saukaka masu. Kwamishinan ’yan sanda na jihar, Alhaji Salisu Abdullahi Fagge ne ya mika cekin kudin ga iyalan mamatan a ranar Laraba da ta gabata, a babban dakin taron […]
Rundunar ’yan sanda a Jihar Sakkwato ta raba wa iyalan ’yan sadan da suka rasa rayukansu a lokacin aiki sama da Naira miliyan 25, domin kawo saukaka masu.
Kwamishinan ’yan sanda na jihar, Alhaji Salisu Abdullahi Fagge ne ya mika cekin kudin ga iyalan mamatan a ranar Laraba da ta gabata, a babban dakin taron hedikwatarsu.
“Yau za mu raba kudi ga iyalan ma’aikatanmu da suka rasa rayukansu a lokacin da suke aiki da hukumar ’yan sanda ta kasa, reshen Jihar Sakkwato domin a taimaki rayuwarsu. Mun tabbata yin hakan zai kara tabbatar masu cewa rundunarmu na sane da su kuma za ta rika taimakonsu a duk lokacin da yin hakan ya ta so.” Inji Kwamishinan.
Ya kara da cewa: “Wadannan kudin da za mu ba su suna cikin wani tsari da hukumar ’yan sanda ta fito da shi na yin asusun ajiya lokacin rayuwa, don bayan ba ka nan su amfani iyalanka. Kan haka ne a yanzu hukamar ta fara da mutum 16, kafin su samu garatitu nasu nan ba da jimawa ba.
“Wannan abin da muka yi a yau, dokar ’yan sanda sashi na 9 karamin sashi na 3, wanda aka yi gyaran fuska a shekarar 2014 ta ba mu damar yin hakan. A wadannan kudin, Naira miliyan 25.046 da za mu raba wa iyalan mamatan; kowannensu zai samu daidai kudin da ya kamata da shi, don mukan raba ne bisa ka’idar girma da shekarun aiki. Sai dai kudin kan kama ne tun daga Naira dubu 500 har zuwa miliyan shida.”
A lokacin rabon wasu mutum uku, wato Sa’idu Isma’il da Gayan Dabid da Emanuel Ubi, iyalansu ba su samu hallarta ba saboda wani uzirin amma takardar kudinsu na ajiye a hannun hukumar.
A karshe Fatima Yahaya ta yi godiya a madadin sauran tare da alkawarin cewa za su sarrafa kudin ta hanyar da ta dace kamar yadda kwamishina ya bukata.